Jihar Gombe da Adamawa sun sanar da ranar bude makarantu

Jihar Gombe da Adamawa sun sanar da ranar bude makarantu

- Da alamun jihohi sun fara samun natsuwa bayan watanni shiga da bullar COVID-19 a Najeriya

- Kusan dukkan jihohin kudancin Najeriya sun sanar da ranar komawa, yayinda wasu tuni sun koma

- Jihohin Arewa maso yamma sun gana don tattauna yadda za a koma karatu

Jihohin Gombe da Adamawa sun shiga jerin jihohin Arewa da suka sanar ranar da daliban firamare, sakandare da jami'a zasu koma karatu bayan kwashe watanni shida.

A jihar Adamawa, gwamnatin ta sanar da ranar 12 ga Oktoba matsayin ranar komawa makaranta.

Gwamnan jihar Ahmadu Fintiri ya bada umurnin haka ne ranar Alhamis a Yola, babbar birnin jihar.

Sakataren yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, yace, "Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2020 matsayin ranar komawa makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar."

"A matsayinmu na gwamnati, zamu yi iyakan kokari wajen tabbatar da an bi ka'idojin kare kai daga cutar COVID-19."

KU KARANTA: Yayinda nike sauraron sunaye daga masu zaben sarki, bari in karanta tarihin nadin sarki a Zazzau - El-Rufa'i

Jihar Gombe da Adamawa sun sanar da ranar bude makarantu

A jihar Gombe kuwa, gwamnatin ta alanta bude makarantun gwamnati da masu zaman kansu ranar 5 ga Oktoba, 2020.

Yayinda makarantun kwana zasu koma ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, dalibai masu jeka ka kawo na firamare, sakandare da Tsangaya zasu koma ranar Litinin 5 ga wata."

Kwamishinan ilimin jihar, Dr Habu Dahiru, ya bayyana hakan a jawabin da yayi.

Yace: "Zango na farko na kakar 2020/2021 zai fara ranar 25 ga Oktoba kuma a kare ranar 18 ga Disamba."

"Yayinda zango na biyu zai fara ranar 10 ga Junairu, 2021 kuma ya karkare 16 ga Afrilu, kuma a fara zango na uku ranar 2 ga Mayu kuma a karkare ranar 6 ga Agusta, 2021."

A bangare guda, Ma'aikatar Ilimi da gwamnatocin jihohi arewa maso yamma bakwai sun gana a Kano domin tattaunawa kan tsarin da zasu zaba na bude makarantu ta hanyar da ba za'a samu matsalan yaduwar cutar COVID-19 ba.

Shirin ilmantar da yara mata watau Girls Education Project (GEP), karkashin asusun lamunin yara na majalisar dinkin duniya UNICEF tare da hadin kan Ofishin FCDO ne suka shirya ganawar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel