Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya

Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya

- Najeriya na cike da jama'a kala-kala kuma mabiya addinai daban-daban

- Amma manyan addinai a Najeriya sune Musulunci da Kiristanci

- Akwai kasaitattun Masallatai da ke a fadin kasar nan inda ake bauta

A kowacce jiha a Najeriya, ba'a rasa masallatai masu kyau.

Musulumci yana daya daga cikin manyan addinai da mutanen Najeriya har da Afirika sukayi imani da shi.

Musulunci ba addini kadai ya shafa ba, hatta gine-ginen Afirika ya shafa. Ana samun Masallatai masu kyau a kowacce jiha a kasar nan.

Ga wasu daga cikin masallai masu kyau dake Najeriya.

1. Masallacin Bashir Uthman Tofa dake Kano

Masallacin Bashir Uthman Tofa yana Gandun Albasa a Kano. An yi wa masallacin wani tsari ne na kwarewa, in da aka kawata shi da kayan ado na alfarma.

Masallacin ya samo sunan shi daga Alhaji Bashir Uthman Tofa, wani dan takarar shugabancin kasa a jamiyya NRC wanda yayi takara a 12 ga watan yuni, 1993.

Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya
Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya. Hoto daga @pulseng
Source: Twitter

2. Babban Masallacin Kano

An mayar da babban masallacin zuwa sabon wuri a shekarar 1582, kuma Abdullahi dan Dabo ya kara ginawa saboda lalacewa da wurin yayi tsakanin 1855 zuwa 1883.

Bayan an rusa shi, gwamnatin turawa ta kara ginawa saboda jin dadin rawar da Najeriya ta taka a WWI.

Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya
Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya. Hoto daga @pulseng
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce

3. Masallacin Kasa dake Abuja, Najeriya

An gina masallacin a cikin babban birnin Najeriya wato Abuja. Masallacin kayattacce ne kwarai.

Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya
Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya. Hoto daga @pulseng
Source: Twitter

4. Babban Masallacin Ilorin

An gina masallacin ne a zamanance a tsakkiyar jihar Ilorin.

Masallacin zai iya daukar kimanin mutane 20,000.

Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya
Hotunan masallatai 4 kayatattu a fadin Najeriya. Hoto daga @pulseng
Source: Twitter

KU KARANTA: Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu

Rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ta tunatar da dukkan arewa rashe-rashen manyan sarakunan da tayi. Za mu waiwaya a kan wasu daga cikin sarakuna da yankin arewa ta yi a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel