Borno: An rasa rayuka 3 a sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram

Borno: An rasa rayuka 3 a sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram

- A ranar Laraba da dare, mayakan Bokao Haram sun shiga kauyen Mandaragraw da ka karamar hukumar Biu ta jihar Borno

- A sakamakon mummunan harin, an rasa rayukan mutum uku sannan mutum bakwai suna samu miyagun raunika

- Kauyen Mandaragraw yana da nisan kilomita 30 zuwa Biu da kuma nisan kilomita 150 zuwa Maiduguri

A ranar Laraba, mayakan ta'addancin Boko Haram sun kai hari yankin kudancin jihar Borno a karamar hukumar Biu.

Kamar yadda majiya daga yankin ta tabbatar, mayakan sun shiga garin Mandaragraw da ke karamar hukumar Biu, inda suka kashe mutum uku har lahira.

Ganau ba jiyau ba ya sanar da cewa, an kai harin kauyen mai nisa kilomita 30 zuwa garin Biu da kuma nisan kilomita 150 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar.

Kamar yadda jaridar The Sun ta bayyana, mayakan ta'addancin sun isa kauyen a kan babura inda suka bude wa farar hula wuta a gidajensu, lamarin da yasa suka tsere zuwa daji.

Auwal Umar, wani mazauni Biu, ya ce, " Sun kai hari da dare inda suka kashe mutum biyu sannan suka raunata wasu bakwai."

An samu makamancin rahoton harin 'yan ta'addan a babbar hanyar Maiduguri zuwa Monguno a ranar Laraba.

Ba a gano aukuwar lamarin ba har sai ranar Alhamis sakamkon barnar da suka yi wa hanyoyin sadarwan yankin. Har yanzu babu cikakken labarin harin.

KU KARANTA: Dauke da tsohon ciki matar aure tayi kundunbala ta fada cikin ruwa domin ceto mijinta da kifi ke shirin cinyewa

Borno: An rasa rayuka 3 a sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram
Borno: An rasa rayuka 3 a sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram. Hoto daga @saharareporters
Source: UGC

KU KARANTA: Masu kwasar kananan yara daga Arewa suna siyarwa a Kudu sun gurfana a kotu

A wani labari na daban, babban kwamandan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, tare da matansa hudu, sun mika kansu ga rundunar sojin kasa ta Najeriya, Channels TV ta wallafa.

Hakazalika, an halaka 'yan bindiga bakwai tare da ceto wasu mutum 8 da aka yi garkuwa da su a Fankama da Sabon Layi da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel