Ba gudu, ba ja da baya: NLC ta lissafa sharudan fasa shiga yajin aiki

Ba gudu, ba ja da baya: NLC ta lissafa sharudan fasa shiga yajin aiki

- Har yanzu 'yan Najeriya ba su daina jin zafin karin farashin litar man fetur da na wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi ba

- Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) ta ce za ta shiga yajin aiki matukar gwamnati ba ta janye karin farashin litar mai da kudin kantarki ba

- A yayin da wa'adin sati biyu da NLC ta bawa gwanati ke dab da cika, kungiyar gwamnoni (NGF) ta kira taron gaggawa

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce halartar zaman sulhu da gwamnatin tarayya ba ya nufin cewa za ta fasa shiga yajin aiki kamar yadda ta sanar tun farko.

A cewar NLC za ta halarci duk wani taro da gwamnati ta gayyaceta domin tattaunawa, amma babu abinda zai hana shiga yaji aiki matukar gwamnati ba ta cika sharudan da ta gindaya mata ba.

A ranar Alhamis ne aka gudanar da taro na biyu a cikin mako guda a tsakanin gwamnati da kungiyar NLC da takwararta ta TUC domin tattauna yadda za a kaucewa shiga yajin aiki.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince a kashe $1.96bn don gina layin dogo daga Kano zuwa jamhuriyar Nijar

NLC da TUC sun fitar da sanarwar fara yajin aiki daga ranar Litinin mai zuwa matukar gwamnati ba ta janye karin farashin man fetur da na wutar lantarki ba.

Ba gudu, ba ja da baya: NLC ta lissafa sharudan fasa shiga yajin aiki
Ba gudu, ba ja da baya: NLC ta lissafa sharudan fasa shiga yajin aiki
Asali: Depositphotos

"Za mu halarci duk wani taro da gwamnati ta gayyacemu amma mu na nan a kan bakanmu na cewa sai an janye karin farashin man fetur da na wutar lantarki, wanda shine sharadi na farko.

DUBA WANNAN: Nasarun Minallah: Sojoji sun kwato sama da mutane 20 daga 'yan bindiga a Katsina

"Bayan hakan mun zo da wasu sharudan da su ka shafi gyaran harkar tattalin arziki. Ba maganar janyewa kadai za mu tattauna ba, akwai wasu sharudan da zamu tattauna wadanda su ka shafi tattalin arziki da kuma yadda za a kiyaye faruwar irin hakan a nan gaba," a cewar shugaban TUC, Quadri Olaleye.

Hatta kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta kira taron gaggawa a ranar Alhamis domin tattauna yadda za a lallashi kungiyar NLC ta fasa shiga yajin aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel