Yanzu-yanzu: Bayan na jihar Kogi, tankar mai ta yi tashin Bam a Legas

Yanzu-yanzu: Bayan na jihar Kogi, tankar mai ta yi tashin Bam a Legas

- Kwana baya bayan na Kogi, an sake mumunar gobarar tankar main fetur a Legas

- Har yanzu ba'a san adadin mutanen da wannan abin ya shafa ba

- Hukumar LASEMA ta kashe wutan kuma na garzaya da mutane asibiti

Wata tankar mai ta yi tashin Bam kuma ta kama da wuta ranar Alhamis a Cele Bus Stop, Iju Ishaga dake jihar Legas kuma mutane da dama sun jiggata, Channels TV ta ruwaito.

Dirakta Janar na hukumar kai agaji na gaggawa na jihar Legas LASEMA, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da aukuwar hakan.

Shugaban LASEMA ya ce jami'ansa na iyakan kokarinsu wajen kashe wutan yanzu haka.

Hukumar a shafinta na Tuwita ta yi bayanin abinda ya faru tare da bidiyon irin bannar da fashewar tankar man tayi.

Jawabin yace: "Yayinda jami'an Tiger Squad suka isa Sakatariyar Alausa, an gano cewa fashewar mai ne. Daga baya da bincike yayi zurfi, an tattaro cewa wata tankar mai ce ta yi hadari kuma ta fashe."

"Hakan ya haddasa gobara a gidajen da ke kusa da wajen kuma motoci sun kone."

"Mutane da dama sun jiggata kuma an garzaya da su asibiti mafi kusa domin jinya."

KU KARANTA: Bude makarantu: Gwamnatocin Arewa maso yamma 7 sun gana da gwamnatin tarayya kan yadda za'ayi

DUBA WANNAN: Minista Sadiya ta auri babban hafsan mayakan Sojin sama, Sadiq Baba

Legit ta kawo muku cewa dalibai biyar daga kwalejin Kogi (KSP) Lokoja, da kananan yara uku, tare da wasu mutane 15 suka mutu a ranar Laraba, sakamakon fashewar tankar man fetur a Lokoja, jihar Kogi.

Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa tankar man ta afkawa wasu motocin a Felele da ke hanyar Lokoja-Abuja, da misalin karfe 8:30am, yayin da wasu motocin ke fada mata.

Tankar man fetur din mallakar kamfanin NNPC, ana hasashen burkinta ya tsinke, inda ta fadawa motici 5, mashina 2 da kekuna 3, yayin ta kashe mutane 23 bayan ta kama da wuta.

Wadanda hatsarin ya rutsa da su akwai daliban kwalejin jihar guda 5, kananan yara 'yan makarantar Nazire guda 3, sai mutane 15, inda suka kone kurmus.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel