APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

- Jam'iyyar APC ta dakatar da hadimin Shugaba Buhari da surikin Bola Tinubu da wasu mutum 8 a jihar Ekiti

- An dakatar da mutanen 10 ne saboda saba dokokin jam'iyyar da suka hada da shigar da jam'iyyar kara a kotu da kuma cacakar gwamnatin Gwamna Kayode Fayemi

- Kafin dakatar da su, jam'iyyar ta kafa kwamitin bincike/ladabtarwa na mutum 10 amma sun ki amsa gayyatar kwamitin inda suka ce ba su yarda da mambobin kwamitin ba

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ekiti ta dakatar da Babafemi Ojudu, mashawarci na musamman na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin siyasa 'saboda saba dokokin' jam'iyya.

A cikin sanarwar da jam'iyyar ta fitar, sakataren watsa labarai, Ade Ajayi ya ce tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Omotune Ojo yana cikin wadanda aka dakatar.

APC ta dakatar da hadimin Buhari da surukin Tinubu a Ekiti
APC ta dakatar da hadimin Buhari da surukin Tinubu a Ekiti. Hoto @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Ojo surukin Bola Tinubu ne, jagora na kasa na jam'iyyar ta APC mai mulki.

Ajayi ya ce an dakatar da mambobin jam'iyyar ne saboda kin janye karar da suka kai jam'iyyar a kotu.

Ojudu da wasu mutum 10 sun yi karar kwamitin gudanarwa na jam'iyyar karkashin jagorancin shugaban APC na Ekiti, Paul Omotosho da kuma yawan cacakar gwamnatin Kayode Fayemi, gwamnan jihar.

Saboda damuwa kan abinda suke aikatawa, APC ta jihar Ekiti ta kafa kwamitin ladabtarwa domin bincikar su.

Amma, sun ki amsa gayyatar kwamitin ta mutum 10 da jam'iyyar ta kafa.

KU KARANTA: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Ta bakin lauyansu, sun rubuta wasika ga shugaban kwamitin ladabtarwar, Sola Ajigbolamu kan cewa ba su gamsu da mambobin kwamitin ba.

Amma cikin wasika mai dauke da kwanan watar 23 ga watan Satumban 2020, Ajayi ya sanar da cewa an dakatar da su har sai masha Allah.

"An dakatar da su ne bisa shawarar kwamitin bincike/ladabtarwa da SEC ta kafa don binciken rashin biyaya da wasu 'yan jam'iyyar suka yi wa NEC a ranar 25 ga watan Yunin 2020 da ta umurnin dukkan mambobin jam'iyyar kada su shigar da kara kotu kuma su janye duk wata kara da suka shigar," a cewar sanarwar.

Sauran wadanda aka dakatar sun hada da Wole Oluyede, Olusoga Owoeye, Dele Afolabi, Ayo Ajibade, Toyin Oluwasola, Akin Akomolafe, Bunmi Ogunleye Femi Adeleye da Bamigboye Adegoroye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel