An yi garkuwa da jigon jam'iyyar PDP a Katsina

An yi garkuwa da jigon jam'iyyar PDP a Katsina

- 'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban matasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a Katsina, Alhaji Ali Sukuntuni

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan sun afka garin ne a safiyar ranar Alhamis suka kuma yi awon gaba da shi

- A ranar Laraba 'yan bindiga sun kuma yi garkuwa da 'yar uwar shugaban wani bankin gwamnatin tarayya, Asiya Musa Dangiwa

An yi garkuwa da jigon jam'iyyar PDP a Katsina
An yi garkuwa da jigon jam'iyyar PDP a Katsina. Hoto @MobilePunchng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Borno: An sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga dadi ne sun yi garkuwa da Alhaji Ali Sukuntuni, jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a garin Rimaye da ke karamar hukumar Kankia na jihar Katsina.

'Yan bindigan sun afka wa garin ne a safiyar ranar Alhami kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Sukuntuni shine tsohon shugaban matasa na jam'iyyar PDP a karamar hukumar.

Ana dai cigaba da garkuwa da mutane da kuma kai hare hare a sassan arewacin Najeriya duk da karin jami'an tsaro da aka tura a yankin.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Idan za a iya tunawa masu garkuwa da mutanen a ranar Laraba sun sace 'yar uwar shugaban wani bankin gwamnatin tarayya a jihar, Asiya Musa Dangiwa.

Thisday ta ruwaito cewa wadanda suka sace Ali sun afka gidansa ne a daren ranar Laraba bayan ya dawo daga unguwa suka bincike gidansa sannan suka yi awon gaba da shi zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Wata majiya daga garin ta bayyana cewa masu garkuwa da mutanen da adadinsu ya kai shida sun shigo garin ne a kan babura suka shiga gidansa suka tafi da shi har kuma yanzu ba su tuntubi iyalansa ba.

Da aka tuntube shi, Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya ce: "Eh, da gaske ne. Na kira DPO ya tabbatar min da afkuwar abin kuma muna kokarin ceto shi."

A wani rahoton, kun ji Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, ta rufe kamfanonin kera magungunan dabobi na jabu a karamar hukumar Bichi na jihar Kano.

Shugaban hukumar na jihar, Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan yayin wata sumame da jami'an hukumar suka kai Laraba a Bichi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel