Bude makarantu: Gwamnatocin Arewa maso yamma 7 sun gana da gwamnatin tarayya kan yadda za'ayi

Bude makarantu: Gwamnatocin Arewa maso yamma 7 sun gana da gwamnatin tarayya kan yadda za'ayi

- Yawancin jihohin kudancin Najeriya sun koma makaranta bayan watanni biyar

- Amma jihohin Arewa basu koma illa yan kalilan na Taraba da Kogi

- Ma'aikatar Ilimi ta baiwa jihohi daman bude makarantunsu

Ma'aikatar Ilimi da gwamnatocin jihohi arewa maso yamma bakwai sun gana a Kano domin tattaunawa kan tsarin da zasu zaba na bude makarantu ta hanyar da ba za'a samu matsalan yaduwar cutar COVID-19 ba.

Shirin ilmantar da yara mata watau Girls Education Project (GEP), karkashin asusun lamunin yara na majalisar dinkin duniya UNICEF tare da hadin kan Ofishin FCDO ne suka shirya ganawar.

Ganawar ta samu halartan dukkan kwamishanonin ilmin jihohin, kwamishanonin lafiya da wasu masu ruwa da tsaki.

Yayin jawabi a zaman, karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce gwamnatin tarayya ta samar da tsari mai sauki da za'a iya amfani da shi wajen bude makarantu.

Ya ce tsarin na bukatar hada karfi da karfen masu ruwa da tsaki domin yiwuwarsa, saboda gwamnatin tarayya, na jiha da na kananan hukumomi na da hakki da rawan takawa.

Gwamna Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Nasiru Gawuna, ya ce gwamnatin jihar ta shirya tsaf domin bude makarantu.

Ya ce an fara wayar da kan shugabannin makarantu kan yadda zasu tabbatar da lafiyan dalibai da malamai.

KU KARANTA: Minista Sadiya ta auri babban hafsan mayakan Sojin sama, Sadiq Baba

Bude makarantu: Gwamnatocin Arewa maso yamma 7 sun gana da gwamnatin tarayya kan yadda za'ayi
Bude makarantu: Gwamnatocin Arewa maso yamma 7 sun gana da gwamnatin tarayya kan yadda za'ayi
Source: Getty Images

Mun kawo muku rahoton cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihohin Legas, Ogun, Osun, Ekiti, da Oyo sun bude ranar Litinin kuma bisa ka'idojin da aka gindaya na kariya daga cutar Korona.

Wakilan jaridar PUNCH sun ziyarci makarantu da dama a yankin kuma sun tabbatar da cewa malamai da dalibai na bin umurnin gwamnati na wanke hannu, amfani da tsummar fuska da baiwa juna tazara.

DUBA NAN: Edo 2020: Buni, Yahaya Bello, Ize-Iyamu sun gana a Abuja don shirya matakin da APC zata dauka

Bayan watanni biyar da kulle makarantun firamare, sakandare da jami'o'i a fadin Najeriya, abubuwa sun dawo daidai yayinda jihohi sun bude makarantu.

Tuni daliban ajujuwan karshe masu jarabawar WAEC da NECO suka koma makaranta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel