Gwamna Buni ya nada hadimai na dandalin sada zumunta 30

Gwamna Buni ya nada hadimai na dandalin sada zumunta 30

- Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya nada sabbin hadimai na dandalin sada zumunta guda 30

- Tunda farko Buni ya nada hadimai 642 hakan ya kawo jimillar hadiman gwamnan zuwa 672

- Sanarwar nadin sabbin hadiman na cikin wata wasika ne mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaran gwamnan Shuaibu Abdullahi

Gwamna Buni ya nada hadimai 30 na dandalin sada zumunta 30
Gwamna Buni ya nada hadimai 30 na dandalin sada zumunta 30. Hoto @daily_trust
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya amince da nadin sabbin mataimakansa na musamman na bangaren dandalin sada zumunta 30 hakan ya kawo adadin hadiman da gwamnan ke da su zuwa 672.

A baya, Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya nada hadimai 642 da suka hada da manyan hadimai na musamman da jami'an tuntuba.

Nadin na cikin wata wasika ce mai dauke da sa hannun Sakataren Watsa labarai na gwamnan, Shuaibu Abdullahi.

KU KARANTA: Gwamnati ta fitar da $1.96bn don ginin layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, kun ji cewa Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, ta rufe kamfanonin kera magungunan dabobi na jabu a karamar hukumar Bichi na jihar Kano.

Shugaban hukumar na jihar, Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan yayin wata sumame da jami'an hukumar suka kai Laraba a Bichi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Muhammad ya ce an kai sumamen ne bayan gano magungunan dabobi na jabu masu yawa na yawo a kaswuwan Sabon Gari da wasu manyan kasuwanni a Kano.

Ya ce hukumar ta kwashe watanni shida tana bincike a kan masu sarrafa magungunan jabun.

Shugaban ya ce jami'an hukumar sun kai sumame kamfanonin a Bichi a ranar Talata sun kuma kwato magunguna na kimanin Naira miliyan 10.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel