Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu

Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu

- Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar EFCC ya yi martani a kan zarginsa da ake da karbar rashawa

- An zargi dakataccen shugaban da sakin wani Aboubakar Hima, dan kasar Nijar bayan ya amshewa tare da kalmashe wasu makuden kudi

- Magu ya bayyana cewa, bai taba karbar cin hanci ba a rayuwarsa kuma duk wanda ya taba bashi ya fito

Dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu, ya musanta zarginsa da ake da karbar cin hanci.

Wannan takardar ta fito ne bayan da dakataccen shugaban EFCC ya fara kare kansa a bisa zarginsa da ake yi da watanda da kudade da kadarorin da aka karbo na gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba.

A yayin martani ga zargin barinn Hima Aboubakar, wani dan kasar Nijar da ya tsere tare da guje wa hukunci, Magu ya ce duk wanda ya taba bashi rashawa ya karba, ya fito ya fallasa.

"Duk wanda ya taba bani rashawa ya fito ya bayyana gaban kwamitin bincike na Mai shari'a Ayo Salami." yace.

Ya jaddada cewa, bai taba karbar rashawa ba a rayuwarsa baki dayanta, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na jam'iyyar APC ya aike wa Obaseki muhimmin sako

Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu
Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu. Hoto daga @lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zamfara: Yadda dan majalisa ya gwangwaje tsoffin malamansa da sha tara ta arziki

A wani labari na daban, Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce da gaggawa zai garzaya bada shaida a kan dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, a gaban kwamitin bincike na fadar shugaban kasa idan an gayyacesa.

Antoni janar na tarayyan yace matukar aka gayyacesa, zai gaggauta zuwa kamar yadda mulkin shugaba Buhari ya horesu da mutunta doka, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: