'Yan daba sun tare matar aure, sun yi awon gaba da takin da take tafe da shi

'Yan daba sun tare matar aure, sun yi awon gaba da takin da take tafe da shi

- Wasu 'yan daba da har yanzu ba a kama ba, sun sassara wata matar aure a gona a jihar Ebonyi

- An gano cewa 'yan daban sun sassarata sannan suka yi awon gaba da takin da taje saka wa gona

- Wasu bayin Allah da suka je wucewa ta gonar ne suka tsinceta sannan suka mika ta asibiti

'Yan daba sun yi wa wata mata illa babba mai suna Chinenye Aroh da ke Agwueziavo a yankin Amaeze da ke Ishiagu ta karamar hukumar Ivo a jihar Ebonyi.

Harin ya auku ne a wani sassa na dajin da ke kusa da wata gona a yankin. An gano cewa 'yan daban sun sassarata ta wuya da hannayenta.

An zargi cewa sun kwashe mata buhunan taki, wanda take da niyyar zuba wa amfanin gonarta.

Sun bar ta a cikin mawuyacin hali kafin wasu masu wucewa su ganta tare da mika ta asibiti, The Nation ta wallafa.

Wani ganau ba jiyau ba, ya yi bayanin cewa lamarin ya faru a sa'o'in farko na ranar Laraba, kuma basu san me ke faruwa ba har hakan ta auku.

"Matar tana nan da ranta. Sun ji mata raunika da adda kuma sun barta ta mutu amma sai wasu mutane suka tsinceta a wani daji da ke Amaeze a Ishiagu," yace.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Loverth Odah, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Ta ce matar ta sanar da 'yan sandan cewa wadanda suka kai mata harin suna wani yare ne na jihar.

KU KARANTA: Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

'Yan daba sun tare matar aure, sun yi awon gaba da takin da take tafe da shi
'Yan daba sun tare matar aure, sun yi awon gaba da takin da take tafe da shi. Hoto daga @Thenation
Source: Getty Images

KU KARANTA: 'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta a kasar Indiya

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke zama a garin Akure, babban birnin jihar Ondo, ta bukaci da a adana mata wasu mutum 7 da ake zargi da zama 'yan daban siyasa daga Ifon.

An kama matasan dauke da miyagun makamai wadanda ake tsammanin za su iya mugun aiki da su a jihar.

Idan za mu tuna, jami'an tsaro sun damke wadanda ake zargin a babban titin Ikaro da ke hedkwatar Ifon a karamar hukumar Ose ta jihar a ranar 19 ga watan Satumba, yayin gangamin zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel