Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 25, mutum 20 sun raunata

Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 25, mutum 20 sun raunata

- Ambaliyar ruwa a jihar Bauchi ta salwantar da rayuka 25 tare da raunata wasu mutum 20

- Kamar yadda mataimakin gwamnan jihar, Baba Tela ya tabbatar, kananan hukumomi 15 haka ta shafa a jihar

- Ya sanar da cewa, ta hannun hukumar NEMA, jihar Bauchi ta samu tallafin kayan abinci da za su kai tirela 220

A kalla mutum 25 ne suka rasa rayukansu bayan ambaliyar ruwan da aka yi a kananan hukumomi 15 na jihar Bauchi a wannan shekarar, The Nation ta wallafa.

A kalla mutum 20 ne suka samu miyagun raunika sakamakon ambaliyar ruwan saman.

Mataimakin Gwamnan jihar, Sanata Baba Tela, ya bayyana hakan bayan karbar jami'ai da yayi daga hukumar tallafin gaggawa (NEMA) ,a gidan gwamnatin jihar da ke Bauchi.

Ya ce kusan N950 miliyan ake bukata domin maye gurbin kadarori, wadanda suka hada da gonaki da sama da gidaje 3,500 da ambaliyar ruwan ta shafa.

Ya ce: "Ina son sanar da cewa, ta hannun NEMA mun samu kayayyakin abinci kala-kala da zasu kai tirela 220 a matsayin kayan tallafi.

"Matsalar ambaliyar ruwan sama ta cigaba da damun jama'ar jihar. A jihar Bauchi, a kalla kananan hukumomi 15 ne hakan ta shafa.

”Muna da sama da gidaje 3,500 da ambaliyar ruwan ta shafa tare da gonaki 2,200. Kuma kun san mun dogara ga noma a wannan yankin.

”A yayin ambaliyar ruwan saman, mun rasa rayuka 25 da kuma wasu 20 sun raunata. Muna ta'aziyya ga iyalansu."

Shugaban hukumar NEMA, wanda ya samu wakilcin Bashir Garga, ya ja kunne a kan yadda ruwan sama ke cigaba a karamar hukumar Zaki ta jihar.

KU KARANTA: 'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta a kasar Indiya

Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 25, mutum 20 sun raunata
Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 25, mutum 20 sun raunata. Hot daga @The Nation
Source: UGC

KU KARANTA: Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata

A wani labari na daban, a kalla mutum 14 suka rasa rayukansu yayin da gidaje masu tarin yawa suka rushe bayan ambaliyar ruwa da ta auku a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara a makon da ya gabata.

Jaridar SaharaReporters ta gano cewa, daruruwan mazauna yankin a halin yanzu sun zama 'yan gudun hijira.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel