Edo 2020: Buni, Yahaya Bello, Ize-Iyamu sun gana a Abuja don shirya matakin da APC zata dauka

Edo 2020: Buni, Yahaya Bello, Ize-Iyamu sun gana a Abuja don shirya matakin da APC zata dauka

- Dan takaran jam'iyyar APC a zaben jihar Edo ya dira Abuja bayan shan kaye ranar Asabar

- Ize-Iyamu ya hadu da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello

Kwanaki uku bayan shan kashi a zaben gwamnan jihar Edo, dan takaran jami'yyar All Progressives Congress APC, Osagie Ize-Iyamu ya gana da jiga-jigan jam'iyyar biyu a Abuja.

Ize-Iyamu ya yi zaman sirri da gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar APC, Mai Mala Buni, da kuma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Wannan shine karo na farko da dan takaran na APC zai fita baynar jama'a tun bayan shan kaye a zaben.

Duk da cewa ba'a bayyana dalilin zaman da sukayi ba kawo yanzu, LEADERSHIP ta tattaro cewa shugabannin na APC sun lallashi Fasto Ize-Iyamu ne ya amince da sakamakon zaben kuma kawai ya hakura.

An yi zaman sirrin ne a ranar Laraba a gidan Mai Mala Buni na Abuja.

Daga baya an samu labarin cewa sun tattauna ne kan mataki na gaba da Fasto Ize-Iyamu zai dauka tunda yanzu ya fadi.

Tuni uwar jam'iyyar APC ta saki jawabi tare da rattafa hannun Mai Mala Buni na taya gwamna Godwin Obaseki, na Peoples Democratic Party (PDP), murnar nasara.

APC ta ce ta amince da sakamakon zaben kuma hakan nasara ne ga Demokradiyya.

DUBA NAN: Mun fara rabawa yan Najeriya tallafin biliyan 11 domin rage radadin cutar Korona - Buhari ga UN

Edo 2020: Buni, Yahaya Bello, Ize-Iyamu sun gana a Abuja don shirya matakin da APC zata dauka
Edo 2020: Buni, Yahaya Bello, Ize-Iyamu sun gana a Abuja don shirya matakin da APC zata dauka
Asali: Facebook

Dazu mun kawo muku rahoton cewa har yanzu ba'a ji kalma ko guda daga bakin tsohon uban gidan Obaseki kuma tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomole ba.

Hakazalika ba'a ji komai daga bakin babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba.

Jagororin biyu sun yi matukar hamayya da Obaseki inda suka bukaci al'ummar Edo suyi watsi da shi.

DUBA NAN NAFDAC ta rufe kamfanonin hada magungunan jabu a Kano

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel