Zargin hadin baki a kan rashin tsaron Zamfara: CNG ta mika korafi ga Buhari

Zargin hadin baki a kan rashin tsaron Zamfara: CNG ta mika korafi ga Buhari

- Wata kungiyar hadin kan arewa ta mika korafi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

- A korafin, ta bayyana yadda ake kama masu assasa rashin satro a Zamfara amma ana sakinsu

- Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasar da ya duba tun kafin lamarin yafi karfin inda ake tsammani

Wata kungiyar hadin kai ta arewa, CNG, ta rubuta korafi ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda take sanar da shi zargin 'yan siyasa da hannun dagula bincike a kan 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Korafin wanda kakakin CNG, AbdulAzeez Suleiman da shugaban kungiyar ta jihar Zamfara. Bilyaminu Aliyu, suka saka hannu, an mika wa manema labarai bayan zanga-zangar da 'yan kungiyar suka yi a ranar Laraba.

Kamar yadda kungiyar tace, wannan hadin kan wurin hana bincike ana zarginsa da taimakawa ayyukan 'yan bindiga da sauran laifuka a jihar Zamfara.

Kungiyar ta ce tana matukar damuwa da zubar jinin da ke faruwa a yankin arewacin Najeriya, hakan yasa ta yanke hukuncin yin kira ga shugaban kasar a kan abubuwan da ke kunshe da kuma abinda zai iya faruwa a nan gaba.

A yayin bada misali, kungiyar ta koka da yadda a ranar 3 ga watan Satumban 2020, wata kotu a Kaduna ta bada umarnin cigaba da tsare wani Abdulmalik Bungudu, wanda ake zargi da hada kai da 'yan bindiga.

"An yanke masa hukunci kuma an kai wanda ake zargin zuwa Gusau amma sai aka bada belinsa, hakan yasa ya tsallake hukuncin.

“A ranar 2 ga watan Satumba, an kama wani Abu Dantabawa yana tattaunawa da 'yan bindiga amma daga bisani sai aka sakesa da wasu mutum 17 da aka kama su tare." Kungiyar tace.

KU KARANTA: Zaben Ondo: Kotu ta adana wasu mutum 7 da ake zargin 'yan daban siyasa ne

Zargin hadin baki a kan rashin tsaron Zamfara: CNG ta mika korafi ga Buhari
Zargin hadin baki a kan rashin tsaron Zamfara: CNG ta mika korafi ga Buhari. Hoto daga @dailynigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

A wani labari na daban, 'yan bindiga da suka kai 20 a ranar Litinin da dare sun shiga kauyen Kana da ke karamar hukumar Nasarawa. Sun kashe mutum daya tare da sace wasu 10 da kuma barin wasu dauke da raunika.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin daga bakin shugaban karamar hukumar Nasarawa, Mohammed Sani Ottos, ya ce 'yan bindigar sun shiga garin da dare, jaridar Vanguard ta wallafa.

Mohammed Ottos ya ce 'yan bindiga sun shiga garin daga tsaunin Kana, kuma sun koma ta wannan hanyar wacce ta bi ta Kana zuwa Maraba Udege, Onda, Agwada, Nasarawa Eggon zuwa birnin Wamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel