Zaben Edo: Amurka ta magantu kan nasarar Obaseki

Zaben Edo: Amurka ta magantu kan nasarar Obaseki

- Kasar Amurka ta taya al'umar jihar Edo murnar fitowa kwansu da kwarkwatarsu suka zabi abunda ransu ya ke so, kuma ta kira zaben sahihi

- Sai dai Amurka ta bayyana damuwarta, kan rahotannin da aka samu na tashe tashen hankula, sayen kuri'u, cin zarafi da wasu laifuka da aka aikata wajen zaben

- Amurka ta ce za ta taimakawa INEC, jami'an tsaro, jam'iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki don gujewa faruwar aikata laifukan zabe a zaben gwamnan Ondo mai zuwa

Kasar Amurka a ranar Laraba ta bayyana zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a makon da ya gabata a matsayin sahihin zabe, kana ta taya al'umar jihar murnar yin zaben cikin lafiya.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka a nan Nigeria, da ofishin ya wallafa a shafukansa na watsa labarai.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince a kashe $1.96bn don gina layin dogo daga Kano zuwa jamhuriyar Nijar

Amurka ta kuma jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da jami'an tsaro bisa kokarinsu, na ganin anyi sahihin zabe ba tare da samun tashin hankula ba.

Zaben Edo: Amurka ta magantu kan nasarar Obaseki
Zaben Edo: Amurka ta magantu kan nasarar Obaseki @PremiumTimesng/@OpportunityDesk
Source: Twitter

Sanarwar ta ce: "Muna taya al'umar jihar Edo murnar gudanar da sahihin zaben gwamnan jihar, kuma cikin kwanciyar hankali.

"Muna godiya ga hukumar zabe ta kasa INEC da hukumomin tsaro, bisa rawar da suka taka a wajen zaben, muna jinjinawa namijin kokarinsu na tabbatar da demokaradiyyar Nigeria.

"Muna ga irin rawar da Gwamna Godwin Obaseki da Pastor Osagie Ize-Iyamu suka taka wajen wanzar da zaman lafiya. Haka suma masu kada kuri'a sun taimaka ta wannan fannin.

"Kasar Amurka ta damu matuka kan rahotannin tashe tashen hankula da aka samu a yayin zaben, kuma akwai rahotannin sayen kuri'u da cin zarafin masu zabe da aka yi.

"Za mu ci gaba da karfafa guiwar masu ruwa da tsaki da suka hada da INEC, jam'iyyun siyasa da jami'an tsaro, kan hanyoyin bunkasa zaben, a zaben gwamnan Ondo mai zuwa."

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a fitar da $1.96bn don gina layin dogo da ya tashi daga Kano-Jigawa-Katsina-Jibia zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Buhari, ya amince da fitar da kudaden ne a ranar Laraba, a yayin zaman majalisar zartaswa ta kasa (FEC) a fadar shugaban kasa, Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel