Gwamnati ta fitar da $1.96bn don ginin layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar

Gwamnati ta fitar da $1.96bn don ginin layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar

- Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da fitar da zunzurutun kudi har Dalla biliyan 1.95 domin ginin layin dogo daga Kano har zuwa Jamhuriyar Nijar

- Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron FEC da Shugaba Buhari ya jagoranta

- Ya kuma ce Majalisar Zartarwar ta amince da ware N3,049,544,000 don ginin na'urar crane da za a rika amfani da shi idan an samu hadarin jirgin kasa

Gwamnati ta fitar da $1.96bn don ginin layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar
Gwamnati ta fitar da $1.96bn don ginin layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar. Hoto daga @BashirAhmaad
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da fitar da Dallar Amurka biliyan 1.95 domin ginin layin dogo da zai tashi daga Kano-Dutse (Jigawa)-Katsina-Jibia zuwa Maradi (Jamhuriyar Nijar).

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yiwa manema labari jawabi a gidan gwamnati bayan taron Majalisar da Shugaba Buhari ya jagoranta a Abuja.

Ya kuma ce Majalisar ta amince da fitar da Naira biliyan 3 don tsarawa, gini, samarwar da gwajin babban na'urar gyara da daukan kaya mai nauyin ton 150 domin ayyukan gaggawa yayin aikin layin dogon.

KU KARANTA: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

"Za a samar da wannan ne domin aiki idan an samu hadari a layin dogon. Za a kashe kudi N3,049,544,000 don samar da shi.

"Wannan shine aiki na farko da aka amincewa Ma'aikatar Sufuri yayin taron.

"Akin na biyu da aka amince da shi shine na kwangilar ginin layin dogo da za ayi daga Kano-Dutse-Katsina-Jibia zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar zuwa kuma Dutse, babban birnin jihar Jigawa a kan kudi $1,959,744,723.71, ciki har da harajin VAT na 7.5% ’’ in ji shi.

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis za ta sake gana wa da Kungiyar Kwadago da Kungiyar masu sana'o'i kan barazanar tafiya yajin aikin da kungiyoyin suka yi kan karin kudin lantarki da man fetur.

Ana sa ran gwamnatin tarayyar za ta bayyana tsarin ta na tallafawa al'ummar kasar yayin taron da za ayi a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel