Tun ranar da Sarkin Zazzau ya rasu, sai na sha magani nake iya bacci - Nasir El-Rufa'i

Tun ranar da Sarkin Zazzau ya rasu, sai na sha magani nake iya bacci - Nasir El-Rufa'i

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana irin halin da ya shiga sakamakon rasuwar Sarkin Zazzau

- Ya ce duk da cewa Obasanjo yace kada suyi bakin ciki, har yanzu zukatansu na ciki da jimami

- Ya yi addu'a Allah ya jikan marigayin kuma yayi masa rahama

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El Rufai, ya bayyana cewa tun ranar marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Abubakar Shehu Idris, ya rasu, ba ya iya bacci sai ya sha ya sha magani saboda tsananin baƙin ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne wajen taron addu'ar sadakar uku na Marigayin da ya gudana yau Laraba, 23 ga Satumba, 2020, BBC ta ruwaito.

Manyan mutane da dama sun halarci taron addu'ar.

Daga cikinsu akwai tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo; Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru; Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong.

KU KARANTA: Mun fara rabawa yan Najeriya tallafin biliyan 11 domin rage radadin cutar Korona - Buhari ga UN

Tun ranar da Sarkin Zazzu ya rasu, sai na sha magani nake iya bacci - Nasir El-Rufa'i
Tun ranar da Sarkin Zazzu ya rasu, sai na sha magani nake iya bacci - Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

A ranar Lahadi, Legit ta kawo muku rahoton cewa Allah ya yiwa Sarkin Zazzau rasuwa.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

DUBA NAN: Kwanaki 3 bayan zabe, har yanzu babu kalma ko guda daga bakin Oshiomole da Tinubu

"Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel