Da duminsa: FG da NLC za su gana ranar Alhamis kan karin kudin man fetur da lantarki

Da duminsa: FG da NLC za su gana ranar Alhamis kan karin kudin man fetur da lantarki

- Hadakar kungiyoyin kwadago na Najeriya za su gana da gwamnatin tarayya a ranar Alhamis domin tattaunawa kan batun karin farashin man fetur da lantarki

- Hakan na zuwa ne bayan kungiyoyin sunyi barazanar tafiya yajin aiki a ranar 28 ga watan Satumba idan har FG ba ta rage farashin ba ko bawa mutane tallafi

- Sanarwar taron ya fito ne daga ofishin jami'in watsa labarai na Ma'aikatar Kwadago da Ayyuka, Charles Akpan inda ya ce a fadar shugaban kasa za ayi taron

Da duminsa: FG da NLC za su gana ranar Alhamis kan karin kudin man fetur da lantarki
Da duminsa: FG da NLC za su gana ranar Alhamis kan karin kudin man fetur da lantarki. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

Gwamnatin Tarayya, FG, a ranar Alhamis za ta sake gana wa da Kungiyar Kwadago, NLC da Kungiyar masu sana'o'i, TUC, a ranar Alhamis kan barazanar tafiya yajin aikin da kungiyoyin suka yi kan karin kudin lantarki da man fetur.

Ana sa ran gwamnatin tarayyar za ta bayyana tsarin ta na tallafawa al'ummar kasar yayin taron da za ayi a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Mataimakin direktan watsa labarai na Ma'aikatar Kwadago da Ayyuka, Charles Akpan ne ya sanar da hakan cikin sakon imel a ranar Laraba kamar yadda The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Sakon ya ce, "Ministan Kwadago da Ayyuka, Dr Chris Ngige zai gana da kungiyoyin kwadago. Za ayi taron ne a ranar Alhamis 24 ga watan Satumban 2020 a Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Kasa da karfe 3 na rana."

FG da kungiyoyin kwadagon sun gana kimanin makonni biyu da suka gabata amma ba a cimma matsaya ba saboda gwamnatin ba ta amince za ta janye karin kudin ba ko kuma bawa mutane tallafi musamman ma'aikata.

Daga bisani NLC da TUC sun sanar da cewa za su fara yajin aiki daga ranar Talata mai zuwa.

Kungiyoyin biyu sun bawa gwamnatin wa'addin makonni biyu ta janye karin idan kuma ba hakan ba su fara yajin aiki.

A wani labarin, Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido-Sanusi, a ranar Talata ya ce 'yan Najeriya suna korafi a kan karij kudin lantarki da aka yi a baya bayan nan ne saboda ba su da tabbacin za su more kudinsu.

Da ya ke jawabi a wurin taron masu saka hannun jari karo na 5 da aka yi a Kaduna, Sanusi ya yi bayanin cewa 'yan Najeriya da dama har da masu treda a shirye suke su biya kudin idan har za a sika samun wutar yadda ya dace domin su inganta sana'ar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel