Kwanaki 3 bayan zabe, har yanzu babu kalma ko guda daga bakin Oshiomole da Tinubu

Kwanaki 3 bayan zabe, har yanzu babu kalma ko guda daga bakin Oshiomole da Tinubu

- Gwamnatin kasar Amurka ya jinjinawa Najeriya kan yadda aka gudanar da zaben jihar Edo

- Shugaba Buhari da uwar jam'iyyar APC ma sun yi nasu tsokaci na alheri

- Amma shine meyasa har yanzu babu kalma ko guda daga bakunan Oshiomole da Tinubu?

Zaben 19 ga Satumba, 2020 na kujerar gwamnan jihar Edo ya zo kuma ya tafi amma har yanzu akwai sauran barbashin kura tsakanin yan siyasa da masu sharhi kan lamuran yau da kullum.

Duk da cewa jam'iyyun siyasa 14 sukayi takara a zaben, sakamakon ya nuna cewa takaran na tsakanin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da All Progressives Congress APC.

A cewar hukumar gudanar da zaben kasa INEC, dan takaran jam'iyyar PDP, Gwamna Godwin Obaseki, wanda ya samu kuri'u 307,955 ya lallasa abokin hamayyarsa, Osaze Ize-iyamu wanda ya samu kuri'u 223,619.

Saboda haka hukumar ta alanta Obaseki a matsayin zakaran zaben.

A ranar Talata kuma, hukumar ta gabatar da shahadar nasarar zabe ga zababben gwamnan da mataimakinsa, Philip Shaibu, a ofishin INEC dake Aduwawa, birnin Benin.

Tuni dai shugaba Muhammadu Buhari ya taya gwamna Obaseki murnar nasarar da ya samu a zaben. Hakazalika uwar jam'iyyar APC ya amince da sakamakon zabe kuma ta taya PDP murna.

DUBA NAN Kotu ta ƙalubalanci Buhari kan miƙa sunayen lauyoyi 11 don mayar da su masu shari'a

Kwanaki 3 bayan zabe, har yanzu babu kalma ko guda daga bakin Oshiomole da Tinubu
Kwanaki 3 bayan zabe, har yanzu babu kalma ko guda daga bakin Oshiomole da Tinubu
Source: Twitter

KU KARANTA: Mun fara rabawa yan Najeriya tallafin biliyan 11 domin rage radadin cutar Korona - Buhari ga UN

Amma duk da haka, har yanzu ba'a ji kalma ko guda daga bakin tsohon uban gidan Obaseki kuma tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomole ba.

Hakazalika ba'a ji komai daga bakin babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba.

Jagororin biyu sun yi matukar hamayya da Obaseki inda suka bukaci al'ummar Edo suyi watsi da shi.

A wani labarin na daban, Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya nuna aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa a zaben shugaban kasa na 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel