Har yanzu akwai jihohi 8 da ba su fara biyan sabon albashi mafi karanci ba - TUC

Har yanzu akwai jihohi 8 da ba su fara biyan sabon albashi mafi karanci ba - TUC

- Kungiyar masu sana'o'i ta Najeriya ta koka kan rashin aiwatar da sabon albashi mafi karanci a wasu jihohi takwas a kasar

- Sanarwar da shugaban kungiyar ya fitar a Legas ya ce za su shiga zanga-zanga tare da kungiyar kwadago idan har gwamnonin jihohin ba su fara biyan albashin ba

- Shugabannin kungiyar sun koka kan yadda gwamnati ke tursasa talakawa su rika rayuwa cikin hakuri amma su kuma suna shagalinsu

Kungiyar Masu Sana'o'i ta Kasa, TUC, ta ce har yanzu akwai jihohi takwas a Najeriya da ba su aiwatar da sabbon tsarin albashi mafi karanci ba da sauran gyare-gyaren da aka yi wa albashin.

Shugaban kungiyar, Quadri Olaleye da Sakataren ta, Musa Ozigi cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Talata a Legas sun ce kungiyar ta rubuta wasika ga gwamnonin jihohin domin tattaunawa da su kan batun amma babu nasara.

Har yanzu akwai jihohi 8 da ba su fara biyan sabon albashi mafi karanci ba - TUC
Har yanzu akwai jihohi 8 da ba su fara biyan sabon albashi mafi karanci ba - TUC. Hoto daga Premium Times
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

Tun a watan Oktoban bara ne gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago suka cimma matsaya kan sabon albashin mafi karanci.

Shugabannin kungiyar sun bayyana damuwarsu kan lamarin sun kuma ce za su hada gwiwa da kungiyar kwadago ta kasa, NLC, wurin yin zanga-zanga da ake shirin yi a ranar 28 ga watan Satumba.

"Babu bukatar mu rika shan wahala irin wannan. Sun ce mu tamke cikin mu amma sun bude nasu.

KU KARANTA: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

"Ba ayi mana ayyuka amma ana tilasta mu biyan kudin da ake kiyastawa. Idan kun tuna wannan gwamnatin ta yi magana sosai a kan tallafin man fetur har ta yi alkawarin gina matattun mai.

"Mun dogara a kan man fetur ne don haka idan an kara kudin fetur zai shafi komai amma dukkan gwamnatocin da suka shude suna karin kudin," a cewar shugabannin kungiyar.

Shugbannin biyu sun sha alwashin yin zanga-zanga kan duk wani tsari da ba zai amfani al'umma ba, sun kuma janyo hankalin gwamnatoci su dauki matakan da ya dace don kaucewa faruwar hakan.

A wani labarin daban, wani dan sanda a yayin zaben gwamnan jihar Edo na shekarar 2020 ya nemi toshiyar baki daga hannun jami'in sa ido a kan zabe na Premium Times a ranar Asabar.

Dan sandan da aka tura ya yi aiki a Okada Junction da ke kan babban titin Sagamu - Ibadan ya tsayar da dan jaridar ya hana shi wucewa duk da ya nuna masa katin shaidar aikinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel