Babbar magana: Ya yiwa tsohuwar budurwarsa ciki, ya sayar da jariran N150,000

Babbar magana: Ya yiwa tsohuwar budurwarsa ciki, ya sayar da jariran N150,000

- Yan sanda sun kama wani matashi mai suna Chijioke Chukwulota kan laifin siyar da jarirai

- Chijioke dai ya yiwa budurwarsa ciki sannan bayan ta haihu sai ya sayar dasu

- Ya siyar da jariran ga wata mai fataucin kananan yara kan N150,000

Rahotanni sun kawo cewa an kama wani mutum mai shekaru 31, Chijioke Chukwulota, kan zargin siyar da wasu tagwaye ga wata mai fataucin kananan yara, Tina Ibeato.

Wanda ake zargin wanda ya kasance dan asalin Imo amma yana zama a Nwewi, jihar Anambra, ya yiwa tsohuwar budurwarsa ciki.

Sai ta haifi tagwaye shine ya siyar da su.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa mai laifin ya siyar da tagwayen ne kan kudi N150,000.

Babbar magana: Ya yiwa tsohuwar budurwarsa ciki, ya sayar da jariran N150,000
Babbar magana: Ya yiwa tsohuwar budurwarsa ciki, ya sayar da jariran N150,000 Hoto: Premium Times/The Nation
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Da zafinsa: Ba ka da hurumin yin haka - Kotu ta ƙalubalanci Buhari kan naɗa masu shari'a

Kakakin yan sanda, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, cewa an kama wanda ya siyar da wacce ta siya.

Ya ce an kuma kwato tagwayen cikin yanayi mai kyau yayinda aka fara bincike.

Ya ce: “a ranar 21 ga watan Satumba da misalin karfe 6:00 na yamma bayan samun bayanai abun dogaro, Jami’an yan sanda sun kama wani mutum mai suna Chijioke Chukwulota mai shekaru 31 na jihar Imo amma yana zama a kauyen Uruagu, Nnewi.

“Wanda ake zargin ya yaudari tsohuwar budurwarsa wacce yayi wa ciki sannan ya sace yaran (tagwaye mata biyu) da ta haifa yan watanni biyu a ranar 4 ga watan Agusta, 2020 bayan ta haife su ta hanyar tiyata.

“Bayan sace yaran sai ya siyarwa da wata Tina Ibeato mai shekaru 32 da yaran kan N150,000.

“A halin da ake ciki an haka wadanda ake zargin su biyu sannan an karbo yaran cikin yanayi mai kyau. Ana kan bincike inda daga bisani za a hukunta su.”

KU KARANTA KUMA: Idan aka bani dama: Ina da burin zama shugaban kasar Nigeria a 2023 - Okorocha

A wani labarin kuma, wani dan Najeriya mai suna Nwoke Agulu a ranar 21 ga watan Satumba, ya wallafa a shafinsa na Twitter yadda ya fasa auren wata budurwa saboda yawan kudin da yaga zai kashe akan auren.

Nwoke yace, duk soyayyarsu ta tashi a tutar banza a lokacin da ta sanar da shi ta kididdigar Miliyan 4 da tayi idan lokacin aurensu yayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel