Mun fara rabawa yan Najeriya tallafin biliyan 11 domin rage radadin cutar Korona - Buhari ga UN

Mun fara rabawa yan Najeriya tallafin biliyan 11 domin rage radadin cutar Korona - Buhari ga UN

- Karon farko, shugabannin kasashen duniya sun gaza zuwa birnin New York halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya

- Kowanne daga cikinsu na jawabinsa ta yanar gizo ga daukacin jakadun kasashe

- Shugaba Buhari ya yi nasa jawabin a ranar Talata, 22 ga Satumba, 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kaddamar da shirin raba tallafin N10.9 billion ga daidakun mutane, kanana da matsakaitan yan kasuwa.

Buhari ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake jawabi ta yanar gizo a taron gangamin majalisar dinkin duniya dake gudana yanzu.

A cewarsa, raba kudin na cikin matakan da gwamnatin ke dauka wajen rage azabar da cutar COVID-19 ta ganawa yan Najeriya.

"Domin rage tasirin a kan Najeriya, gwamnatinmu ta kaddamar da raba kudi N10.9 Billion ga daidaikun iyalai, kanana da matsaikaitan yan kasuwa matsayin tallafi," Yace

A jawabinsa, shugaban kasa ya jaddada jajircewan gwamnatin Najeriya wajen hadin kai da sauran kasashe domin jin dadin yan Najeriya.

Bugu da kari, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ya kafa asusun lamunin biliyan 500 domin bada tallafi da tabbatar da jin dadin talakawa, yayinda bankin CBN ta kaddamar asusun lamunin N3.5 tiriliyan domin karfafa masana'antu.

Taken taron gangamin bana na majalisar dinkin duniya shine 'Rana goben da muke so, muke bukata: Hada karfi da karfi wajen yaki da cutar Coronavirus.'

DUBA WANNAN LABARIN: Zulum ya cika alkawari, ya baiwa iyalan kwamandan Sojan da aka kashe N20m

Mun fara rabawa yan Najeriya tallafin bilyan 11 domin rage radadin cutar Korona - Buharii ga UN
Mun fara rabawa yan Najeriya tallafin bilyan 11 domin rage radadin cutar Korona - Buharii ga UN
Source: UGC

KARANTA WANNAN: Garar N30 a Kano: Bayan shekara daya, gidan cin abincin ya kasa cigaba da aiki

Ga yadda za a yi a samu wannan jari:

1. Mai bukatar jari zai shiga shafin yanar gizo na https://www.survivalfund.ng ko kuma http://www.survivalfundapplication.com.

2. Idan mutum ya shiga wannan shafi sai ya nemi inda ake yin rajista domin neman rukunin tallafin da zai shiga.

Rukunin wadanda ake ba tallafi

• Sahun farko na wadanda ake ba tallafi a tsarin MSME su ne ‘yan kasuwan da su ka gaza biyan ma’aikatansu a watanni uku da su ka wuce.

Gudumuwar tallafin albashin da za a bada a nan ya na tsakanin N30, 000 ne zuwa N50, 000.

• Sahu na biyu su ne masu ma’adanai da kamfanonin da su ke hada abubuwa.

• Sahu na uku su ne kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa.

3. Daga nan sai mutum ya zabi sahun da zai shiga

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel