Zulum ya cika alkawari, ya baiwa iyalan kwamandan Sojan da aka kashe N20m

Zulum ya cika alkawari, ya baiwa iyalan kwamandan Sojan da aka kashe N20m

- Yadan bi yadin, hannu da hannu, Zulum ya mika chek na milyan 20 ga iyalan marigayi Kanar Bako

- Zulum ya siffanta kwamandan a matsayin jarumin Soja

- Ya baiwa iyalan sauran Sojojin da aka kashe tare da shi kashi daya cikin goman abinci iyalansa suka samu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya cika alkawarinsa na kyautan naira milyan ashirin da ya yiwa iyalan jarumin kwamandan da aka kashe a filin yaki da yan ta'addan Boko Haram.

Gwamnan ya sanar da hakan da safiyar Laraba, a shafinsa na Tuwita da Facebook.

A ranar Litinin ne rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Bayan Kanar Dahiru Chiroma Bako da aka kashe, Zulum ya sanar da baiwa iyalan sauran Sojoji uku da aka kashe tare da shi milyan biyu-biyu.

"Na samu labarin cewa akwai Sojoji uku da suka rasa rayukansu tare da Kanar Bako, saboda haka, na bada kyautar kudi milyan biyu ga iyalan kowanne cikinsu," Zulum yace.

Zulum ya cika alkawari, ya baiwa iyalan kwamandan Sojan da aka kashe N20m
Zulum ya cika alkawari, ya baiwa iyalan kwamandan Sojan da aka kashe N20m
Source: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi

A jiya Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da bawa mata da 'ya'yan marigayi Kanal Dahiru Chiroma Bako kyautar gida da kudi Naira miliyan ashirin (N20m).

Farfesa Zulum ya sanar da hakan ne ranar Talata yayin jana'izar marigayi Kanal Bako wacce aka yi a makabartar sojoji ta Maimalari da ke Maiduguri jihar Borno.

Yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin jana'izar, Farfesa Zulum ya ce; "Kanal Bako jarumin soja ne marar tsoro, saboda kokarinsa ne har yanzu mayakan Boko Haram su ka gaza cimma Damboa.

"Domin walwalar iyalinsa, gwamnatin jihar Borno ta amince da bawa iyalinsa tallafin miliyan N20, takardar fitar da kudin daga banki za ta shiga hannun matarsa a yau da yamma ko gobe da safe," cewar Zulum.

"Na ji an ce Kanal Bako bashi da gidan kansa kafin ya rasu, a saboda haka gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin ginawa iyalinsa gida. Kanal Bako bai mutu a banza ba, a saboda haka ba zamu manta da iyalinsa ba."

"Ba zamu taba mantawa da irin kokarinsa ba, Allah ne kadai zai yi masa sakayya, Allah ya gafarta masa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel