Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 8 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20

Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 8 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20

- Rasuwar marigayi sarkin Zazzau, Shehu Idris, ta tono mikin zukatan jama'ar arewacin Najeriya

- A cikin shekaru 20 da suka wuce, yankin arewa ya yi rashin manyan sarakuna adalai

- An rasa Sarki Ado Bayero, Dakta Usman Kabir, Muhammadu Maccido Abubakar da sauransu

Rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ta tunatar da dukkan arewa rashe-rashen manyan sarakunan da tayi. Za mu waiwaya a kan wasu daga cikin sarakuna da yankin arewa ta yi a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Alhaji Dakta Shehu Idris

Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20
Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20. Hoto daga Abdulaziz Umar
Source: Facebook

An haifa marigayin mai martaban a watan Maris na 1936. Sunan mahaifinsa Malam Idrisu amma an fi saninsa da Auta.

Ya karba sarautar Zazzau a ranar 8 ga watan Fabrairun 1975 bayan rasuwar Sarki Muhammadu Aminu.

Sarkin shine na 18 da aka taba yi a masarautar Zazzau, kuma yafi kowanne a sarakunan Zazzau dadewa a karagar mulki. Ya rasu a ranar 20 ga watan Satumbar 2020 yana da shekaru 84.

Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido Abubakar

Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20
Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20. Hoto daga BBC
Source: Getty Images

KU KARANTA: Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

An haifi Muhammadu Macciɗo Abubakar a ranar 20 ga watan Afrilu 1926 a jihar Sokoto a Najeriya.

An haifi marigayin a ranar 20 ga watan Afirilun 1926 a jihar Sokoto. Mahaifinsa Siddiq Abubakar III ya yi Sarki Musulmi na tsawon shekaru 50 kafin rasuwarsa a 1988.

Ya hau karagar mulkin yana da shekaru 70 a shekarar 1996. Sarki Muhammadu Maccido shine Sarkin Musulmi na 19 a kasar.

Basaraken ya rasu a hatsarin jirgin sama na ADC wanda ya tashi daga Abuja zuwa Sokoto a ranar 28 ga watan Oktoban 2006.

Alhaji Ado Bayero

Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20
Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20. Hoto daga BBC
Source: Getty Images

An haifa Sarkin Kano Ado Bayero a watan Yulin 1930. Mahaifinsa shine Alhaji Abdullahi Bayero wanda yayi sarautar Kano na shekaru 27.

An nada shi sarautar Dabo a ranar Juma'a 11 ga watan Oktoban 1963 bayan rasuwar Sarki Muhammadu Inuwa Abbas.

Ya hau sarautar Dabo yana da shekaru 33 sannan ya yi mulki na shekaru 51.

Ya rasu a ranar 6 ga watan Yuni 2014 yana da shekaru 84 a duniya. Ya bar mata hudu da 'ya'ya sama da 60 da jikoki 300.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta musanta bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna

Sarkin Katsina Dakta Muhammad Kabir Usman

Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20
Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20. Hoto daga BBC
Source: Facebook

An haifa marigayin a shekarar 1928. Ya gaji mahaifinsa Usman Nagogo wanda ya mulki jihar Katsina daga shekarar 1944 zuwa 1981.

Marigayin shine Sarkin Fulani na 10 kuma Sarkin Sullubawa na 3. A lokacinsa ne aka kirkiri jihar Katsina daga jihar Kaduna.

Ya rasu a ranar 8 ga watan Maris na 2008 yana da shekaru 80 a duniya. Ya rasu ya bar mata uku da yara da yawa.

Sarkin Daura Muhammadu Bashar

An haifa Muhammadu Bashar a shekarar 1926 a garin Daura. Dan asalin gidan sarauta ne. Kakansa shine Sarkin Daura na 58 kuma ya shafe tsawon shekaru.

Muhammadu Bashar shine sarkin Daura na 59. Ya rasu a ranar 25 ga watan Fabrairun 2007 bayan shekaru 41 yana mulki.

Sarkin Gombe Shehu Usman Abubakar

Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20
Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20. Hoto daga BBC
Source: Facebook

Sarki Usman Abubakar ne Sarkin Gombe na 10, kuma ya yi zamaninsa daga watan Janairun 1984 zuwa watan Mayun 2014.

Ya rasu a ranar 27 ga watan Mayun 2014. Ya rasu yana da shekaru 76 da haihuwa kuma ya yi mulkin shekaru 30 bayan gadar mahaifinsa da yayi.

Lamiɗon Adamawa Dakta Aliyu Mustapha

Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20
Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 7 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20. Hoto daga BBC
Source: Facebook

An haifa marigayi Lamidon Adamawa a 1922 kuma ya hau karagar mulkin a ranar 26 ga watan Yulin 1953.

Ya karba sandar mulkin daga hannun Gwamna Sir Bryan Sherwood-Smith. Ya shafe shekaru 57 a kan karagar mulki.

Lamido Aliyu Mustapha ya rasu a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2010 yana da shekaru 88 a duniya.

Sarkin Bauchi Sulaiman Adamu

An haifa Marigayi Sarkin Bauchi, Alhaji Sulaiman Adamu a ranar 77 ga watan Janairun 1993. Shine Sarkin Bauchi na 10 kuma ya rasu a ranar 23 ga watan Yulin 2010 bayan kwashe shekaru 28 yana mulki.

Ya rasu ya bar matan aure huɗu da 'ya'ya 19.

A wani labari na daban, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Lahadi ya shugabanci ministoci da manyan jami'an gwamnati zuwa kasar Zazzau domin wakiltar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wurin jana'izar Sarkin Zazzau.

Daga cikin wakilan akwai ministar kudi, kasafi da tattali, Zainab Ahmed, ministan muhalli, Dr. Mahmud Mohammed da ministan sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika.

Hakazalika, daga cikin wakilan shugaban kasan akwai mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel