Gwamnati, 'yan sanda da kungiyar kwadago sun bukaci mutanen Katsina su kare kansu daga 'yan bindiga

Gwamnati, 'yan sanda da kungiyar kwadago sun bukaci mutanen Katsina su kare kansu daga 'yan bindiga

- Rundunar 'yan sanda, kungiyar kwadago da gwamnatin Katsina ta shawarci mutane su rika kare kansu daga 'yan bindiga

- An yi wannan kirar ne wurin wani taron tattaunawa na kwana guda da aka yi cikin bikin makon 'yan jarida a Katsina na 2020

- Wakilan gwamnati, 'yan sanda da kungiyar kwadagon sun ce aikin tsaro ba na hukumomin tsaro bane kawai saboda haka mutane na iya kafa kungiyoyi don kare kansu

Mahalarta wani taron rana guda da aka yi a ranar Litinin a Katsina sun bukaci mazauna jihar su rika kare kansu duk lokacin da 'yan bindiga ko wasu miyagu suka kai musu hari.

Sun roki mutane su dena bari sai aikin samar da tsaro a hannun jami'an tsaro su kadai kamar yadda The Punch ta ruwaito.

'Yan sandan Katsina sun bukaci mutane su kare kansu daga harin 'yan bindiga
'Yan sandan Katsina sun bukaci mutane su kare kansu daga harin 'yan bindiga. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Wadanda suka yi jawabi a wurin taron tattaunawar da kungiyar 'yan jarida na jihar Katsina ta shirya cikin bikin makon 'yan jarida na 2020 sun hada da sakataren gwamnatin jihar, SSG, Alhaji Musa Inuwa da mashawarcin gwamna Masari na musamman kan tsaro, Mallam Ibrahim Katsina.

Saura sun hada da shugaban kungiyar kwadago na jihar, Mallam Hussaini Hamisu da Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah.

SSG din ya ce, "Lamarin tsaro hakki ne da ya rataya kan kowa. Gwamnatocin tarayya da jiha suna iya kokarinsu don kawar da 'yan bindiga da sauran masu laifi, ya dace mutane suma su bada nasu gudunmuwar don tallafawa hukumomin tsaro.

"Mutane za su iya kafa kungiyoyi suyi rajista. Duk da cewa DPO na 'yan sandan unguwanni za su rika kula da ayyukan kungiyoyin. Idan kun fita waje aikin sintiri kun dawo da safe, sai ku tafi wurin DPO ku kai masa rahoto."

KU KARANTA: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

Inuwa ya kuma kalulabalanci 'yan jarida su rika bincike mai zurfi akan dalilin da yasa har yanzu ake fama da hare-haren duk da irin kokarin da gwamnatocin tarayya da jiha ke yi.

A bangarensa, mashawarcin gwamnan ya ce, "Masu aikata laifukan nan ba aljannu bane, suna nan cikin mutane. Mun san cewa da hadin kan mutane za mu ga bayan miyagun."

Kakakin 'yan sandan na Katsina ya bukaci mutane su rika jarumta suna taimakawa hukumomin tsaro da bayani a kan miyagu da ke unguwanninsu.

A wani labarin daban, wani dan sanda a yayin zaben gwamnan jihar Edo na shekarar 2020 ya nemi toshiyar baki daga hannun jami'in sa ido a kan zabe na Premium Times a ranar Asabar.

Dan sandan da aka tura ya yi aiki a Okada Junction da ke kan babban titin Sagamu - Ibadan ya tsayar da dan jaridar ya hana shi wucewa duk da ya nuna masa katin shaidar aikinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel