Zaben Ondo: Kotu ta adana wasu mutum 7 da ake zargin 'yan daban siyasa ne

Zaben Ondo: Kotu ta adana wasu mutum 7 da ake zargin 'yan daban siyasa ne

- Wata kotun majistare da ke zama a Akure ta bukaci a adana wasu 'yan daban siyasa 7 a gidan gyaran hali

- Kamar yadda daraktar gurfanarwa ta jihar ta sanar, an kama su ne da miyagun makami da suka hada da bindgigi tare da harsasai

- An zargesu da fakewa da gangamin siyasa amma suna tada hankulan jama'a kafin zuwa zaben gwamnan jihar da za a yi

Wata kotun majistare da ke zama a garin Akure, babban birnin jihar Ondo, ta bukaci da a adana mata wasu mutum 7 da ake zargi da zama 'yan daban siyasa daga Ifon.

An kama matasan dauke da miyagun makamai wadanda ake tsammanin za su iya mugun aiki da su a jihar.

Idan za mu tuna, jami'an tsaro sun damke wadanda ake zargin a babban titin Ikaro da ke hedkwatar Ifon a karamar hukumar Ose ta jihar a ranar 19 ga watan Satumba, yayin gangamin zabe.

Daraktan gurfanarwa, Grace Olowoporoku ta sanar da kotun cewa, wadanda ake zargin an kama su da bindigogi miyagu tare da harsasai.

Ta tabbatar da cewa, hakan ya yi karansatye da dokokin jihar na hana ajiye makamai, lamarin da yasa ta bukaci mai shari'ar da ya bada umarnin adana wadanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun, Mai shari'a Tope Aladejana, ya bada umarnin adana mutum bakwai da ake zargin a gidan gyaran hali har sai an kammala bincike a kan laifin da ake zarginsu da shi.

Antoni janar kuma kwamsihinan shari'a na jihar, Adekola olawoye, ya ce hakkin gwamnati ne tabbatar da bada kariya ga jama'arta.

Olawoye ya zargi wadanda aka kaman da kokarin yawo da miyagun makami a cikin jihar da sunan gangamin siyasa.

An dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Oktoban 2020.

KU KARANTA: Tsohuwa 'yar shekara 57 da ta kammala JS3 na sakandare tace tana so ta zama ma'aikaciyar lafiya

Zaben Ondo: Kotu ta adana wasu mutum 7 da ake zargin 'yan daban siyasa ne
Zaben Ondo: Kotu ta adana wasu mutum 7 da ake zargin 'yan daban siyasa ne. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sanata Ali Ndume ya koka akan kisan Kanal din soja da 'yan Boko Haram suka yi a Borno

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke garin Dutse a jihar Jigawa a ranar Laraba, ta bada umarnin adana mata wani makaho mai shekaru 60 mai suna Muhammad Abdul.

Ana zarginsa da yunkurin yin luwadi da dan jagorarsa, lamarin da yasa aka bukaci adanasa a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun majistaren mai suna Akilu Isma'il, wanda ya umarci a adana masa Abdul a gidan gyaran halin, ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel