Saurayi ya tsere bayan budurwarsa ta yanke masa kudin aure har N4m

Saurayi ya tsere bayan budurwarsa ta yanke masa kudin aure har N4m

- Wani dan Najeriya, Nwoke Agulu ya ce yayi takardun karya na asibiti saboda ya kubuce wa wani biki da zai ja ya kashe Miliyan 4

- Budurwar da yake tarayya da ita ta ce sai ya fara biyan Miliyan daya saboda ta siya suturun da zatayi amfani dasu wurin bikin

- Takardun asibitin na bogi sun nuna shi AS ne, wanda hakan zai hanashi auren budurwar a lafiyance

Wani dan Najeriya mai suna Nwoke Agulu a ranar 21 ga watan Satumba, ya wallafa a shafinsa na Twitter yadda ya fasa auren wata budurwa saboda yawan kudin da yaga zai kashe akan auren.

Nwoke yace, duk soyayyarsu ta tashi a tutar banza a lokacin da ta sanar da shi ta kididdigar Miliyan 4 da tayi idan lokacin aurensu yayi.

A cewar sa, matar ta ce zai fara tura mata Miliyan 1 a asusun bankin ta domin siyan kayan anko.

Mutumin yace don ya guje wa hakan, sai ya garzaya asibiti aka yi masa takardun bogi da ke nuna shi AS ne, dama yasan ita budurwar AS ce. Sanin cewa mutane biyu masu AS basa aure don haka sai suka hakura da juna.

Wannan wallafar tasa ta jawo cece-kuce in da daruruwan jama'a sukayi ta sukarsa.

Akwai mutanen da suka yi ta ce masa dama ya sanar da ita gaskiyar lamarin ba wai yayi mata karya ba.

Akwai wadanda sukace zuwa yin takardun bogi shi kanshi laifi ne a shari'ance.

KU KARANTA: Budurwar da mahaifiyarta za ta mutu ta shirya aurenta cikin kwana 5, an daura aurenta a cikin asibiti

Saurayi ya tsere bayan budurwarsa ta yanke masa kudin aure har N4m
Saurayi ya tsere bayan budurwarsa ta yanke masa kudin aure har N4m. Hoto daga Nwoke
Source: Twitter

KU KARANTA: Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan

A wani labari na daban, Toluwase Kembi budurwa ce mai shekaru 20 da ke karantar fannin kasuwanci a makarantar gaba da sakandare ta Ilaro da ke jihar Ogun.

An tabbatar da cewa ta mutu bayan saurayinta da take zuwa wurinsa a yankin Ikorodu ta jihar Legas ya kasheta.

A makonni kadan da suka gabata ne aka nemi budurwar aka rasa bayan ta je yi wa wani Owolabi Yusuf girki, wanda babban malami ne kuma saurayinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel