Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

- Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su dena koka wa game da farashin lantarki idan an musu bayanin da yadda ya dace

- Sanusi ya ce al'umma ba su da tabbas cewa za su samu wata riba ko alfano daga karin kudin shi yasa suke korafi

- Ya yi bayanin cewa idan har mutane da masu sana'o'i sun cewa karin kudin lantarkin zai haifar musu samun riba a sana'o'insu ba za su ki biya ba

'Yan sanda sun ce mutanen gari su kare kansu daga harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun ce mutanen gari su kare kansu daga harin 'yan bindiga a Katsina. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido-Sanusi, a ranar Talata ya ce 'yan Najeriya suna korafi a kan karij kudin lantarki da aka yi a baya bayan nan ne saboda ba su da tabbacin za su more kudinsu.

Da ya ke jawabi a wurin taron masu saka hannun jari karo na 5 da aka yi a Kaduna, Sanusi ya yi bayanin cewa 'yan Najeriya da dama har da masu treda a shirye suke su biya kudin idan har za a sika samun wutar yadda ya dace domin su inganta sana'ar su.

Sanusi ya ce, "A kan batun karin kudin wutar lantarki, gwamnati ba ta yi wa mutane bayani ta yadda za su gamsu bane.

"Ya kamata mutane su fahimta, idan kaga ana kukan karin kudin wutar lantarki, ana kallonsa ta bangare daya ne. Kamata ya yi a rika aka duba cewa ana bukatar lantarki domin sarrafa kayayyaki, sana'a da sauransu.

KU KARANTA: Zaben Edo: Yadda dan sanda ya nemi in bashi toshiyar baki - Mai sa ido kan zabe

"Ka duba irin kudin da za ka samu. Akwai banbanci tsakanin wanda ya ke amfani da lantarki amma baya tsinana komai da shi da wanda ya ke samun kudi.

"Mutane za su biya ko nawa ne idan sun san cewa za su iya samun kudi daga lantarkin. Mutane suna kuka ne saboda suna biyan kudin lantarki amma ba su samun kudi daga lantarkin.

"Idan ka tafi kauye ka sayar da kilowatt daya kan N100 kuma treda ya san cewa zai samu ninkin kudin sau hudu, ba zai ji kyashin biya ba."

Tsohon sarkin ya kuma ce ya kamata gwamnati ta rika yin ayyuka a wuraren da zai kawo cigaban tattalin arzikin al'umma.

A wani labarin daban, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi karin haske a kan dangartakarsa da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Da ya ke magana a shirin Morning Show na Arise TV, Obaseki ya ce ba shi da matsala yin takara da Ize-Iyamu a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumban 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel