'Yan bindiga sun kashe basarake a Filato

'Yan bindiga sun kashe basarake a Filato

- Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe hakimin Feron, Bulus Chuwang Jang a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Plateau

- Rundunar 'yan sandan jihar ta bakin kakakinta, Ubah Ogaba ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige basaraken har lahira

- Kakakin 'yan sandan ya ce tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya tura jami'ai zuwa garin da nufin binciko wadanda suka aikata kisar da kama su

'Yan bindiga sun kashe hakimin Feron a karamar hukumar Barkin Ladi na jihar Plateau, Bulus Chuwang Jang a harin da suka kai da yammacin ranar Litinin.

Shugaban matasan Berom a Heipang da ke makwabtaka da Barkin Ladi, Rwang Tengwong ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin a Jos a ranar Talata.

'Yan bindiga sun kashe basarake a Filato
'Yan bindiga sun kashe basarake a Filato. Hoto daga The Punch
Source: UGC

DUBA WANNAN: Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)

Tengwong ya ce, "Mun rasa daya daga cikin manyan shugabanni a Barkin Ladi sakamakon harin 'yan bindiga. Shine hakimin rikon kwarya na Foron, Da Bulus Chuwang Jang. 'Yan bindiga sun harbe shi ya mutu a jihar Litinin a kusa da Shen."

Mataimakin shugaban karamar hukumar Barkin Ladi, Pam Chollom shima ya tabbatar da kisar da aka yi wa basaraken inda ya ce sun kira taron gaggawa a kan lamarin.

Ya ce, "Eh, da gaske ne 'yan bindiga sun kashe daya daga cikin masu sarautar gargajiyar mu. Abin bakin ciki ne kuma muna tir da hakan. A halin yanzu muna taro a kan lamarin. Zan sanar da kai matakin da muka dauka idan mun gama."

DUBA WANNAN: Zulum ya yi alhinin rasuwar Kanar Bako, Kwamandan sojin da Boko Haram ta kashe a Borno

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ubah Ogaba ya ce an shigar da rahoton afkuwar lamarin a ofishinsu.

A cewarsa, Kwamishinan 'yan sandan jihar ya aike da jami'ai zuwa karamar hukumar domin bincike kan abinda yayi sanadin kisar basaraken da kamo wadanda suka aikata kisar.

Ogaba ya ce, "Mun samu rahoton cewa 'yan bindiga sun kashe basaraken kuma an fara bincike a kan lamarin."

A wani labarin daban, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya yi wa Rundunar Sojin Najeriya ta'aziyyar rasuwar Kanar Dahiru Bako da ya mutu sakamakon harin kwantan bauna da Boko Haram suka yi wa sojoji a Borno.

An kai wa Mista Bako hari ne a ranar 20 ga watan Satumba tare da tawagarsa yayin wani sintiri da suka tafi a Sabon Gari - Wajiroko a karamar hukumar Damboa. Read more:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel