Zaben Edo: Obaseki ya ce ba shi da matsala da Ize-Iyamu

Zaben Edo: Obaseki ya ce ba shi da matsala da Ize-Iyamu

- Zababben gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa ba shi da wata matsala da abokin hamayyarsa da ya kayar Osagie Ize-Iyamu

- Gwamnan ya ce amma akwai wasu mutane a tsohuwar jam'iyyarsa ta APC da ya ke da matsala da su

- Obaseki ya samu nasararsa karo na biyu a kan Ize-Iyamu a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumba da kuri'u 307,955

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi karin haske a kan dangartakarsa da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Da ya ke magana a shirin Morning Show na Arise TV, Obaseki ya ce ba shi da matsala yin takara da Ize-Iyamu a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumban 2020.

DUBA WANNAN: Zulum ya yi alhinin rasuwar Kanar Bako, Kwamandan sojin da Boko Haram ta kashe a Borno

Zaben Edo: Obaseki ya ce ba shi da matsala da Ize-Iyamu
Zaben Edo: Obaseki ya ce ba shi da matsala da Ize-Iyamu. Hoto daga ThisDay
Source: Twitter

Amma gwamnan ya ce yana da matsala da wasu mutane a jam'iyyar ta APC da suka kusa da dan takarar ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole.

A hirar da aka yi da shi a BBC a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba bayan an sanar shine ya lashe zaben, gwamnan ya fada wa Ize-Iyamu cewa mutane sun nuna masa cewa lokaci ya yi da zai tafi ya yi wani abin daban.

An ranstar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya yi nasara a kananan hukumomi 13 cikin 18 na jihar Edo da kuri'u 3017,955.

KU KARANTA: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

A jawabin da ya yi yayin hirar da aka yi da shi a wata shirin gidan talabijin na Arise, Obaseki ya ce yana fatan za su sulhunta da dan takarar na APC.

Gwamnan ya ce:

"Ba wannan ne karo na farko da na yi takara da Osagie Ize-Iyamu ba. Ashirye na ke muyi aiki tare idan ya tuntube ni, za mu iya tattaunawa.

"A gani na ba shine matsalar ba. Mutanen da ke kusa da shi ne matsalar, wadanda suka zuga shi ya koma APC. Ba ni da matsala da shi."

A wani labarin, kun i cewa an nada tsohon jami'in tuntuba na Majalisar Tarayya, Sanata Muhammad Abba-Aji a matsayin Sakataren kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta Gabas, NEGF.

Abba-Aji ya rike mukamin jami'in tuntuba a majalisar tarayya a zamanin mulkin shugaban kasa Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel