An gano dalilin da yasa sojan da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa

An gano dalilin da yasa sojan da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa

- An gano dalilin da yasa sojan da ke yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabas ya kashe kansa a ranar Alhamis da ta gabata

- Sojan ya shiga garin Damaturu inda ya siyo waya wacce daga bisani aka gano ta sata ce kuma ta wani babban soja

- A gaban jama'a babban sojan ya ci mutuncinsa yayin da wasu suka nadi bidiyon lamarin, hakan ta sa ya kashe kansa

A ranar Alhamis da ta gabata ne wani sojan da ke yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabas, ya kashe kansa.

Jaridar ta gano cewa, sojan mai mukamin Lance Corporal Victor Ojeamiran, ya kashe kansa bayan wani babansa ya zargesa da laifin sata a gaban abokan aikinsa, wani abokin aikinsa ya tabbatar wa da Premium Times.

Ojeamiran ya kashe kansa bayan ya mika wata wasika ga shugabansa wanda za a bai wa babban sojan da ya tozarta shi, wata majiya ta tabbatar yayin da ta nemi aboye sunanta.

Wasikar ta kare kai ce wacce sojan ya bada domin bayanin cewa bashi da hannu a cikin satar, Premium Times ta gano.

Abinda ya faru shine, marigayin ya je Damaturu da ke jihar Yobe kuma ya siyo wayar da aka taba amfani da ita. Majiyar ta ce a rashin saninsa, an saci wayar ne daga wani babban soja a Damaturu.

Babban sojan ya bibiyi wayar inda ya kama ta a hannun marigayin yayin da yake kan hanyar zuwa inda yake aiki a Buni Gari, bayan siyanta da yayi.

An zargi cewa, babban sojan ya ladabtar da marigayin a bainar jama'a yayin da mazauna yankin suka dinga nadar bidiyon suna wallafawa a shafukansa na sada zumunta.

KU KARANTA: Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

An gano dalilin da yasa sojan da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa
An gano dalilin da yasa sojan da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa. Hoto daga Premium Times
Source: Twitter

KU KARANTA: Abubuwa 5 da Obaseki ya fadi kafin zaben jihar Edo

Ojeamiran ya kasa hakuri da wannan bidiyon cin zarafin na zargin sata, kuma ba a bashi damar kare kansa ba, majiyar ta tabbatar.

Ya sanar da abokan aikinsa cewa, bai san me zai sanar da matarsa da 'ya'yansa ba a kan bidiyon kuma an ci masa mutunci a kan laifin da bai aikata ba a idon duniya.

Daga nan ya yanke shawarar kashe kansa bayan komawarsa wurin aiki.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar, Sagir Musa, ya ce har yanzu bai samu labari a kan wannan lamarin ba kuma baya Yobe a halin yanzu.

Amma ya tabbatar da cewa an cigaba da binciken a kan lamarin.

A wani labari na daban, wani soja da ke yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabas ta Najeriya ya kashe kansa, The Cable ta ruwaito.

Majiyoyi sun sanar da cewa, sojan mai mukamin lance corporal da ke aikinsa a Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe, ya kashe kansa a ranar Alhamis yayin da yake bakin aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel