Gwamna Babagana Umara Zulum ya nada sabon Sarkin Biu

Gwamna Babagana Umara Zulum ya nada sabon Sarkin Biu

- Bayan mako guda, an nada sabon sarkin Biu a jihar Borno

- Gwamna Zulum ya nada dan sarkin da ya rasu, Mai Aliyu Mustapha

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya tabbatar da zabin Mai Mustapha Umar Mustapha a matsayin sabon sarkin masarautar Biu.

Sabon sarkin zai gaji mahaifinsa, marigayi Mai Umaru Mustapha, wanda ya rasu ranar 16 ga Satumba, 2020.

Yayin gabatar da takardar nadin ga sabon sarkin ranar Litinin, Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Jidda, ya taya shi murnar zabenshi na masu zaben sarki sukayi.

Mataimakin gwamnan, Usman Umaru Khadaru, ya bada takardar ga sabon sarkin a gaban kwamitin zaben sarki dake fadar Biu.

Zaku tuna cewa tsohon sarkin Biu, Mai martaba Umar Mustapha Aliyu, ya rasu ne daren Litinin, 14 ga Satumba, 2020.

Ya rasu a daren Litinin a asibitin gwamnatin tarayya dake Gombe, bayan gajeruwar rashin lafiya.

A cewar Iyalan marigayin, sun bayyana cewa: "Mun yi rashin ginshikin masarautar Biu da jihar Borno gaba daya, Sarkin Biu.”

”Allah ya gafarta kura-kuransa kuma ya azurtashi da gidan Aljannah Firdawsi mafi girma.”

Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu ya hau mulkin masarautar ne a shekarar 1989.

KU KARANTAN WANNAN: Jihohi sun yi watsi da gwajin cutar Korona; Legas, Abuja, Kano da Ogun kadai ke yi yanzu

Gwamna Babagana Umara Zulum ya nada sabon Sarkin Biu
Gwamna Babagana Umara Zulum ya nada sabon Sarkin Biu
Asali: Facebook

Shin ka Karanta Wannan labarin: Dalibai a jihohin kudu sun koma makaranta, na Arewa na zaune a gida

A bangare guda, Rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Ado Isa, kakakin rundunar atisayen Lafiya Dole, ya ce Kanal Bako ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa tawagarsa harin kwanton bauna yayin da suka fita sintiri.

Domin sauke manhajarmu a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel