Jihohi sun yi watsi da gwajin cutar Korona; Legas, Abuja, Kano da Ogun kadai ke yi yanzu

Jihohi sun yi watsi da gwajin cutar Korona; Legas, Abuja, Kano da Ogun kadai ke yi yanzu

- Jihohin Najeriya sun fara watsi da gwajin cutar Coronavirus da ta addabi duniya

- Shugaban hukumar yaki da cutar ya ce yan Najeriya su saurari hauhawar adadin sabbin masu kamuwa

- Mutane su daina tunanin cutar Korona ta kare, cewar Chike Ihekwaezu

Dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, Dr Chike Ihekweazu, ya ce za'a samu tashin masu kamuwa da cutar Korona saboda bude makarantu da tashohin jiragen sama da ake yanzu.

Saboda haka, ya gargadi mutane su kawar da tunanin cewa cutar ta kare.

Yayinda jawabi a taron hira da manema labarai da kwamitin PTF ta saba a Abuja, Ihekwaezu ya ce Legas, Abuja, Ogun da Kano kadai suke gwajin cutar Korona akai-akai.

Musamman, Ihekwaezu ya ce an rage gwaji sosai a Taraba, Adamawa, Kogi, Nasarawa, Niger, Kebbi, Zamfara, Jigawa da yobe.

Ya ce yan Najeriya basu son fitowa a gwadasu kuma ana bukatar gwaji domin kawo karshen annobar.

Yace. "Ina da tabbacin abinda ke faruwa a Legas, Abuja, Ogun, kuma watakila Kano da wasu yan tsirarun jihohi."

"Bugu da kari, yanzu da ake bude makarantu da tashohin jirgi, ya kamata mu kara kaimi wajen gwajin mutane saboda da yawa zasu kamu."

KU KARANTA: Dalibai a jihohin kudu sun koma makaranta, na Arewa na zaune a gida

Jihohin sun yi watsi da gwajin cutar Korona; Legas, Abuja, Kano da Ogun kadai ke yi yanzu
Jihohin sun yi watsi da gwajin cutar Korona; Legas, Abuja, Kano da Ogun kadai ke yi yanzu
Asali: Facebook

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta ce ta baiwa jihohi daman bude makarantu kuma su ke da zabin lokacin da zasu bude.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana hakan ranar Alhamis, 17 ga Satumba, yayin amsa tambayoyi a hira da manema labaran kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da COVID-19 kamar yadda aka saba.

Ministan ya ce tuni gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi daman bude makarantunsu. Amma Nwajuiba ya ce wajibi ne gwamnatocin jihohi su bi sharrudan kare dalibai da cutar COVID-19 da gwamnatin tarayya ta gindaya.

DUBA NAN Jerin Jihohi 4 da zasu bude jami'o'i da makarantunsu a watan nan

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel