Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi

Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi

- Kensmith Rechiel matashi wanda Najeriya ke alfahari dashi sakamakon kirkire-kirkirensa

- Yaro ne mai karancin shekaru wanda ya kirkiri babur da jirgin sama mai daukar mutum daya da jirgin kasa

- Kensmith ya fara bayyanar da fasaharsa tun yana dan shekara 7 da haihuwa a duniya

Babu shakka, Najeriya tana cike da matasa masu dumbin kwazo da fasaha. Za'a iya cewa, har yanzu akwai masu fasaha da dama a Najeriya wadanda ba'a riga an farga dasu ba.

Kensmith Rechiel wani yaro ne mai cike da abin mamaki wanda ya kirkiri abubuwa da dama. Ya kirkiri babur, jirgin sama mai daukar mutum daya, jirgin kasa mai daukar mutane biyu har da mota mai amfani da remote duk kafin ya cika shekaru 18 da haihuwa.

An haifi Kensmith ne a Umuebo Umuezeala Owerre a karamar hukumar Ehime Mbano a jihar Imo. Shi ne yaro na 6 a cikin su yara 10 da Allah ya azurta iyayenshi dasu. Ya fara bayyanar da fasaharshi tun yana da shekaru 7 da haihuwa.

A lokacin da ya cika shekaru 16 da haihuwa ya kirkiri jirgin sama wanda ya sa ma suna "Donko King".

Yayi suna ne bayan bidiyon shi ya karade yanar gizo wanda aka ganshi yana tuka babur din da ya kirkira da kanshi.

Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi
Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi
Source: Facebook

KU KARANTA: Soja da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wasika mai ratsa zuciya

A wata hira da jaridar Legit.ng tayi dashi, wacce Duru Victor ya ruwaito, Kensmith wanda bai dade da gama karatunsa na makarantar sakandare ba, yace rashin kudi da madafa yasa ya fara kirkire-kirkire.

Ya kara bayani, inda yake cewa rashin aikin mahaifinsa da kuma yadda duk yan uwansa suka dogara da sana'ar kosan mahaifiyarsa sune dalilan da suka sa ya kara dagewa akan kirkire-kirkiren.

Yace, "Na gano baiwata a lokacin da nake da shekaru 7 da haihuwa kuma tun daga nan na dage wurin kirkiro jiragen sama da kasa da kuma mota mai remote tare da kuma babur, wanda ban dade da kirkirarshi ba.

"Babbar matsalata yanzu haka ita ce rashin kudi. Inayin ayyuka kanana saboda in samu yadda zanyi in kirkiro abubuwa."

Duk da rashin kudi da iyayensa suke fama dashi, suna iya kokarinsu wurin taimaka mishi wurin cika burinshi. Yana da burin zama injiniya mai sarrafa jiragen sama.

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai sabon hari Magumeri, sun halaka mutum 3

Yaro mai shekaru 11 mai suna PJ Brewer-Laye, ya zama jan gwarzo bayan da ya dauka matakin da kowanne mai hankali zai iya dauka wurin ceto rayuwar kakarsa mai suna Angela.

Kakarsa ta fara korafin jiri, rashin karfin jiki da kuma disashewar gani, amma babu wanda zai taimaka a gidan.

Kamar yadda jaridar New York Post ta wallafa, a lokacin da tsohuwar ta fara jin jikinta babu dadi, ta fito inda ta jingina da wata alama da ke kan titi sannan jikanta da ke wasa ya hangota.

"Ina jingine da wata alama a kan titi amma sai kawai ga jikana. Ina duban dama na hango motata kirar kamfanin Mercedes Benz tana tunkaro ni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel