Dakarun soji sun damke fitaccen dan sara-suka da 'yan kungiyarsa 10 a Jos

Dakarun soji sun damke fitaccen dan sara-suka da 'yan kungiyarsa 10 a Jos

- Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kamen wani gagarumin dan bindiga a jihar Filato

- Hussaini Isah, shugaban 'yan sara-suka na Jos ya shiga hannu tare da mukarrabansa 10

- Kamar yadda kwamandan runduna ta musamman ya sanar, ba za su tsagaita ba har sai sun ga karshen masu laifi

Runduna ta musamman ta sojin Najeriya da ke tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato, ta damke wani Hussaini Isah, wanda ta ce shine shugaban Sara-suka, wata kungiya da ta dade tana barna a yakin karamar hukumar Jos ta arewa.

Hakazalika, an cafke wasu mambobi 10 na kungiyar, Vanguard ta wallafa.

Manjo janar Chukwuemeka Okonkwo, kwamandan rundunar ta musamman, wanda ya kai samamen a ranar Asabar a Jos, ya ce sun kama su a yankin Gangare.

Okonkwo ya ce wannan kamen babban nasara ce a cikin kokarinsu na ganin an kawar da miyagu daga Jos.

"Ba za mu tsagaita ba har sai kananan laifuka, kashe-kashe da duk wani nau'in rashin tsaro sun yi kaura daga Jos.

"Wadannan sune wadanda ake zargi da dukkan laifuka tare da tada zaune tsaye a Jos. Sun kashe rayuka da dama kuma suna da matukar hatsari ga jama'a.

"Tabbas, mun tura rundunarmu, amma samamen da suka kai yankin ya matukar taka rawar gani wurin dakile laifuka," yace.

KU KARANTA: 'Yar uwar Boko Haram: Yadda rundunar soji ke matsanta wa Darul Salam

Dakarun soji sun damke fitaccen dan sara-suka da 'yan kungiyarsa 10 a Jos
Dakarun soji sun damke fitaccen dan sara-suka da 'yan kungiyarsa 10 a Jos. Hpto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Zaben Edo: Tattara komatsanka ka bar jihar Edo - 'Yan sanda ga Wike

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta ce tana sake matsanta wa Darul-Salam domin tabbatar da cewa duk wata barazana daga kungiyar ta kaura, Daily Trust ta tabbatar.

Shugaban fannin yada labarai na tsaro, Manjo janar John Enenche, ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyi daga manema labarai yayin zantawar mako-mako a kan ayyukan rundunar a Abuja.

Rundunar sojin ta bankado wasu iyalai 290 daga kungiyar Darul-Salam tare da sansaninsu da maboyarsu da ke Koton Karfe a jihar Kogi da wasu sassa na jihar Nasarawa.

Sun kai samamen ne bayan wasu mutum 410 sun mika kansu daga kungiyar a Toto da ke jihar Nasarawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel