Zaben Edo: 'Yan daban da ke yi wa PDP aiki sun yiwa matar shugaban jam'iyyar mu duka - APC (Hotuna)

Zaben Edo: 'Yan daban da ke yi wa PDP aiki sun yiwa matar shugaban jam'iyyar mu duka - APC (Hotuna)

- Jam'iyyar APC a jihar Edo ta yi ikirarin cewa 'yan daban jam'iyyar PDP sun yi wa matar shugaban APC na Egor mugun duka

- Jam'iyyar ta APC ta wallafa wasu hotuna da ta ce na matar ne a lokacin da aka kai ta asibiti ma'aikatan jinya suna mata magani

- Sanarwar ta APC ta fitar a shafin ta na Twitter ya ce 'yan daban sun taho za su kwace kayan zabe ne a rumfar zabe ta Tipper Garage amma matar ta hana sai suka mata duka

Zaben Edo: APC ta yi ikirarin an yi wa matar shugaban jam'iyyar ta duka, an garzaya da ita asbiti
Zaben Edo: APC ta yi ikirarin an yi wa matar shugaban jam'iyyar ta duka, an garzaya da ita asbiti. Hoto daga Edo State APC
Source: Twitter

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo ta yi ikirarin cewa 'yan daba da ke yi wa jam'iyyarPeoples Democratic Party (PDP) aiki sun yi wa matar shugaban ta na Egor duka.

Jam'iyyar ta APC ta yi ikirarin cewa an mata duka ne saboda ta yi jayayya da 'yan daban da suka zo rumfan zaben da nufin tada tarzoma kamar yadda The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

DUBA WANNAN: Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter @EdoStateAPC, jam'iyyar ta saka hotuna masu yawa na matar da ake yi wa duka a lokacin da wasu ma'aikatan jinyar asibiti ke mata magani.

Sakon ta suka wallafa a Twitter ya ce: " Yan daban @OffcialPDPNig sun kwace kayyakin zabe a rumfar zabe ta Tipper Garage da ke Egor. Matar shugaban jam'iyyar mu ta yi kokarin hana su amma suka mata mugun duka. An garzaya da ita zuwa asibiti mafi kusa."

Majiyar Legit.ng Hausa ba ta tabbatar da inda asibitin ya ke ba.

A wani labarin daban, Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa, NAPTIP, a Kano ta kama wata matar aure mai shekaru 29, Jamila Abubakar kan kashe dan kishiyarta, Mohammed Bashir.

Kwamandan NAPTIP na Kano, Shehu Umar ya ce an kama wacce ake zargin ne a ranar Alhamis, bayan ta yi wa yaron duka har sai da ya mutu a kusa da kasuwar Tarauni a Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel