'Yan bindiga sun afka wurin shaƙatawa a Kogi, sun kashe mutum ɗaya sun raunta da dama

'Yan bindiga sun afka wurin shaƙatawa a Kogi, sun kashe mutum ɗaya sun raunta da dama

- Wasu 'yan bindiga su uku sun kai hari wani wurin shakatawa a jihar Kogi sun kashe mutum daya sun raunata wasu da dama

- An kai harin ne a yammacin ranar Juma'a a Karamar hukumar Dekina misalin karfe 7.45 na yamma a cewar 'yan sanda

- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ayuba Ekpeji ya ce ya baza jami'ansa cikin gari na nufin kamo maharan su fuskanci hukunci

'Yan bindiga su uku sun kai hari wani wurin shakatawa mai suna Royal Garden Relaxation Spot da ke Egume a karamar hukumar Dekina na jihar Kogi a ranar Juma'a sun kashe mutum ɗaya sun raunta wasu a cewar 'yan sanda.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa 'yan bindigan sun afka wurin shakatawar sun bude wuta misalin karfe 7.45 na yammacin ranar Juma'a.

Yan bindiga sun afka wurin shakatawa a Kogi, sun kashe mutum daya sun raunta da dama
Yan bindiga sun afka wurin shakatawa a Kogi, sun kashe mutum daya sun raunta da dama
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

Sanarwar da kakakin 'yan sandan DSP William Aya ya ce maharan sun tsere bayan kai harin.

Sanarwar bai fayyace ko 'yan bindigan sun yi wa mutane fashi ba amma DPO na Dekina ya aike da jami'ansa wurin ba tare da bata lokaci ba bayan samun rahoton abinda ya faru.

"An tarar da gawar wani mutum kwance cikin jininsa sannan aka dauke shi zuwa wani asibiti da ke kusa inda aka tabbatar da mutuwarsa.

"An bar gawarsa a asibitin domin ayi gwajin gano musababbin mutuwarsa," a cewar sanarwar.

Kazalika, sanarwar ta ce Kwamishinan 'yan sanda, Mista Ayuba Ekpeji ya aike da jami'ansa domin bin sahun maharan.

KU KARANTA: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Ya bada tabbacin cewa za a kamo wadanda suka kai harin a kuma gurfanar da su a kotu.

Kwamishinan ya shawarci mutane su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a wuraren da suke su kuma shigar da rahoto game da duk wani abu da ba su gamsu da shi ba a wurin hukuma.

A wani rahoton, rundunar ƴan sandan jihar Gombe a ranar Alhamis ta yi holen wani manomi mai shekaru 37 mai suna Ephraim Kadiri da ake zargi da kashe wani ɗan acaɓa a Gombe.

Da ya ke gabatar da wanda ake zargin a hedkwatar hukumar, kwamishinan ƴan sanda, Shehu Maikuɗi ya ce wanda ake zargin ya sace babur ɗin ɗan acaɓan ya sayar N120,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel