Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo

Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo

- Ana fargabar cewa an harbi wani mutum a wurin kada kuri'a a Ologbo a jihar Edo

- Basaraken Ologbo, Jason Owen Akenzua ya tabbatar da cewa ya ji karar harbin bindiga

- Akenzua ya kuma ce ya tuntubi DPO na 'yan sanda amma ya fada masa 'yan sanda ne suka yi harbin don tarwatsa mutane

Rahotanni da ke fitowa daga karamar hukumar Ikpoba Okah na jihar Edo sun bayyana cewa an harbi wani mutum daya da bindiga a Ologbo.

Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo
Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo
Source: Original

DUBA WANNAN: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

Da aka tuntube shi game da harbin da aka ce an yi a Ologbo Dukedoom, Enogie, Mai martaba Jason Owen Akenzua ya ce ya ji karar harbin bindiga kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Amma tuntubi DPO na 'yan sanda an fada masa cewa 'yan sanda ne su kayi harbi a lokacin da wurin zaben ya rincabe.

'Na ji karar harbin bindiga kuma na kira DPO na Ologbo a waya. Ya ce min 'yan sanda ne suka yi harbi don tarwatsa wasu mutane da ke neman tada hayaniya a wurin. Hankula sun kwanta a wurin yanzu." ya ce.

KU KARANTA: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

A wani labarin kun ji an kama wani mai gidan haya, David Ntiero Okon saboda banka wa yar hayarsa wuta a Calabar, jihar Cross Rivers saboda ta gaza biyan kudin haya N11,000.

Abin ya faru ne a ranar Laraba a gida mai lamba 9, Ansa Ewa Street a garin Cobham da ke Bayside a Calabar ta Kudu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun ce mai gidan ya zuba fetur a dakin Misis Mary Samuel sannan ya kuna wuta wadda ya yi sanadin konewar dakin na matar da kayan da ke ciki.

Wani ganau da mai gadi da ke zaune a gidan hayan da ya ce sunansa Obongette ya Mary na wacce ta yi kimanin shekaru bakwai a gidan hayar ta kasa biyan mai gidan bashin N11,000 ne saboda hare-haren da masu tada kayan baya ke kaiwa wurin sana'ar ta na sayar da kifi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel