Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

- Wani mai gida ya kona yar hayarsa saboda yana bin ta bashin N11,000 daga cikin kudin haya

- Mai gidan ya tambayi cikon kudinsa ne amma ta ce masa ya bata kwana daya ta sayar da kifi sannan ta bashi

- Ya bari ta shiga bandaki wanka ya zuba fetur a dakinta da ta dawo kuma ya kuna wuta ya rufe kofa har sai da ta mutu

An kama wani mai gidan haya, David Ntiero Okon saboda banka wa yar hayarsa wuta a Calabar, jihar Cross Rivers saboda ta gaza biyan kudin haya N11,000.

Abin ya faru ne a ranar Laraba a gida mai lamba 9, Ansa Ewa Street a garin Cobham da ke Bayside a Calabar ta Kudu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mai gida ya banka wa 'yan haya wuta saboda N11,000
Mai gida ya banka wa 'yan haya wuta saboda N11,000. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Rahotanni sun ce mai gidan ya zuba fetur a dakin Misis Mary Samuel sannan ya kuna wuta wadda ya yi sanadin konewar dakin na matar da kayan da ke ciki.

Wani ganau da mai gadi da ke zaune a gidan hayan da ya ce sunansa Obongette ya Mary na wacce ta yi kimanin shekaru bakwai a gidan hayar ta kasa biyan mai gidan bashin N11,000 ne saboda hare-haren da masu tada kayan baya ke kaiwa wurin sana'ar ta na sayar da kifi.

Ya ce, "A ranar Laraba matar ta dawo daga siyo kifi a Oron da ke jihar Akwa Ibom da yamma sai mai gidan ya ce ta biya shi cikon bashin N11,000 na kudin haya da ya ke binta. Ta fada masa bata da kudi a lokacin amma ya bari idan ta sayar da kifin za ta biya.

Obongette ya kara da cewa, "Rokon alfarmar da matar ta yi ya fusata mai gidan inda yace bata son biyan kudin ne. Da matar ta tafi bandaki yin wanka, mai gidan ya zuba fetur a dakin ta. Bayan ta fito wanka ta shiga aki sai ya kuna wutar ta mamaye dakin.

"A lokacin da matar ta yi kokarin fitowa daga dakin, mutum ya rufe kofar ya kuma dako adda ya rika korar mutanen da suka yi yunkurin kawo mata dauki yana barazanar zai kashe su."

KARANTA NAN: Yanzu-yanzu: FG ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan sanarwar cike sabon fom din banki

Ya ce bayan matar ta mutu, mutanen unguwar taru suka dauki gawar ta suka kai gidan mai gidan hayar suka ajiye.

"A jiya (Alhamis) 'yan sanda sun zo sun kama mutumin sun dauke gawar domin mutumin ya yi yunkurin tserewa amma mutane sun hana shi guduwa. Mahaifinsa ne ya gina gidan," in ji Obongette.

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Irene Ugbo ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kara da cewa an kama mai gidan an kuma kai gawar wurin ajiya a asibiti.

Ta ce, "Ana bincike domin gano ainihin abinda ya faru."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel