Haramta shiga Amurka kan magudi: Kada ku raina mana wayo - Gwamnatin tarayya

Haramta shiga Amurka kan magudi: Kada ku raina mana wayo - Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana bacin ranta kan jawabin da gwamnatin kasar Amurka da Birtaniya suka saki kan zaben gwamnan jihar Edo da za'a gudanar gobe da na Ondo da za'a gudanar ranar 10 ga Oktoba.

Gwamnati ta nuna rashin amincewarta kan haramtawa wasu yan siyasa samun bizan shiga Amurka saboda zargin tafka magudi a zaben Kogi da Bayelsa da akayi a 2019.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya a ranar Juma'a ta saki jawabin cewa gwamnatin Najeriya ba zata lamunci irin wannan abu da Amurka da Birtaniya ke kokarin yi ba.

Ma'aikatar ta yi bayanin cewa akwai dokokin da Najeriya ta gindaya domin hukunta masu tafka magudi da rikici a zabe.

Amma, gwamnatin tarayya ta baiwa Amurka da Birtaniya shawaran cewa abinda ya kamata shine su hada kai da hukumomi ta hanyar taimaka musu da hujjoji saboda ita ta dau matakin da ya dace.

KU KARANTA: Jihar Ebonyi aka aurar da kananan yara mata a Najeriya - Gwamnatin tarayya

Haramta shiga Amurka kan magudi: Kada ku raina mana wayo - Gwamnatin tarayya
Haramta shiga Amurka kan magudi: Kada ku raina mana wayo - Gwamnatin tarayya
Asali: UGC

KU KARANTA: Wajibi ne ku baiwa mutum sauran 'Data' da bai karasa ba inda ya siya wani ko tayi esfiya - NCC ga kamfanonin sadarwa

Jawabin yace, "Zai zama tamkar rainin wayo da cin mutuncin yancin Najeriya ga wasu daga waje su yiwa yan kasarmu hukunci tare da hukuntasu ta hanyar haramta musu biza haka kawai."

"Gwamnatin tarayya, musamman shugaban kasa, yana iyakan kokarinsa wajen baiwa hukumomin tsaro abubuwan da suke bukata na kudi, kayan aiki domin tabbatar da ingancin zabe."

"Yayinda muke mika godiya ga gudunmuwar abokanmu musamman gamayyar kasashen Turai, muna kira ga kasar Birtaniya da Amurka su hada kai da hukumominmu ta hanyar basu hujjojin da suka samu na magudi domin hukuntasu da doka,"

Daga karshe, gwamnatin tarayya ta na yiwa Amurka fatan alkhairi kan zaben shugaban kasarsu dake tade.

A bangare guda, Gwamnatin jihar Kogi ta aike wasikar martani ga gwamnatin kasar Amurka kan haramtawa gwamnan jihar, Yahaya Bello, shiga kasarta sakamakon zargin cewa ya yi magudin zaben gwamnan jihar a Nuwamban 2019.

A wasikar da ta aikewa Jakadan kasar Amurka a ranar 16 ga Satumba, 2020, gwamnatin ta ce kamata yayi Amurka ta baiwa gwamnan damar kare kansa kuma ba zata amince ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel