Yanzu-yanzu: Yan sanda sun yiwa masaukin gwamna Wike zobe a Edo

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun yiwa masaukin gwamna Wike zobe a Edo

- Yayinda ake shirin zabe gobe, jami'an tsaro sun hana gwamna Wike fita daga masaukinsa

- Gwamnonin APC da PDP sun dira jihar Edo domin taimakawa jam'iyyunsu wajen nasara a zaben gobe

- Shugaban uwar jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya ce an takurawa gwamnonin PDP dake jihar

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta na kuka kan zoben da jami'an hukumar yan sanda suka yiwa masaukin gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a Benin, babbar birnin jihar Edo.

Wike, wanda shine shugaban yakin neman zaben gwamnan jihar Edo na jam'iyyar PDP, ya dira jihar yayinda ake shirin zaben gobe.

A jawabin da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Rivers, Akawor Desmond, ya saki, ya ce kimanin yan sanda 300 sun zagaye masaukin da gwamnan yake zaune.

Ya ce yayinda gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da Hope Uzodinma ke yawo yadda suka ga dama amma an hana Wike fita.

DUBA NAN: Haramta shiga Amurka kan magudi: Kada ku raina mana wayo - Gwamnatin tarayya

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun yiwa masaukin gwamna Wike zobe a Edo
Yanzu-yanzu: Yan sanda sun yiwa masaukin gwamna Wike zobe a Edo
Source: Depositphotos

"Mutan jihar Ribas sun samu labarin cewa an yiwa masaukin da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ke zaune a garin Benin, jihar Edo da ya tafi aiki." Jawabin yace.

"Zaku tuna cewa gwamna Wike aka nada shugaban yakin neman zaben PDP na zaben gwamnan Edo, irin kujerar da gwamna Ganduje na Kano ke rike da shi na APC."

"Gwamna Ganduje da gwamna Hope Uzzodinma na Imo na Benin, jihar Edo suna yiwa APC aiki ba tare da wani tsangwama ko cin mutunci ba."

"Kumar jami'an tsaro sun saba alkawarin da sukayi, sun fara cin mutuncin gwamna Wike da bai yi laifin komai"

Yayinda aka tuntubi kakakin yan sandan jihar Rivers, Chidi Nwafor, ya ce bai da labarin abinda ya faru.

Uche Secondus, shugaban uwar jam'iyyar PDP, ya ce jami'an tsaro na hana gwamnoninsu sakatawa a jihar Edo.

KARANTA NAN: Wajibi ne ku baiwa mutum sauran 'Data' da bai karasa ba inda ya siya wani ko tayi esfiya - NCC ga kamfanonin sadarwa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel