Jihar Ebonyi aka fi aurar da kananan yara mata a Najeriya - Gwamnatin tarayya

Jihar Ebonyi aka fi aurar da kananan yara mata a Najeriya - Gwamnatin tarayya

- Sabanin tunanin da ake cewa Arewa aka fi aurar da yara mata, gwamnatin tarayya ta ce kudu ne

- Jihar Ebonyi na daya daga cikin jihohin da kananan yara suka fi zuwa gidan miji

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihar Ebonyi, daya daga cikin jihohin yankin kabilar Igbo na cikin jihohin da aka fi aurar da kananan yara mata a Najeriya.

Gwamnati ta yi kira ga gwamnan jihar, David Umahi, ya dakile wannan lamari saboda shugaba Muhammadu Buhari ya damu matuka kai.

Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta bayyana hakan ne yayinda ta kai ziyara jihar Ebonyi ranar Juma'a.

Ta ziyarci jihar ne domin kaddamar da shirin rabawa mata rishon girki mai amfani da iskar gas 13,000 ga matan karkara.

DUBA NAN: Wajibi ne ku baiwa mutum sauran 'Data' da bai karasa ba inda ya siya wani ko tayi esfiya - NCC ga kamfanonin sadarwa

Jihar Ebonyi aka aurar da kananan yara mata a Najeriya - Gwamnatin tarayya
Jihar Ebonyi aka aurar da kananan yara mata a Najeriya - Gwamnatin tarayya
Source: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa an gudanar da shirin ne a Onueke, karamar hukumar Ezza ta kudu a jihar.

Tace, "diya mace na kan gaba wajen tsare-tsaren shugaban kasa kuma ina kira gareta ta bamu hadin kai."

"Ilmantar da diya mace shine abu mafi muhimmanci da gwamnati da iyali zasu iya kuma hakan ya sa gwamnatin tarayya ke kashe kudade da yawa wajen ilmantar da diya mace."

"Hakazalika, maganar aurar da yara mata ya zama ruwan dare a kasar, kuma jihar Ebonyi har yanzu na daya daga cikin jihohi na gaba."

"Saboda haka ina rokon cewa a magance wannan lamari kuma hanyar yin haka shine tabbatar da cewa yara na zuwa makarantun firamare da jami'a," Ta kara.

Gwamna Umahi ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr Kelechi Igwe.

KU KARANTA: Bayan shekaru 14 ana gini da rikicin hana ginawa, an kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a kasar Greece

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel