Haramta shiga Amurka kan magudi: Ba zan amince da hakan ba - Gwamnan Kogi ya mayarwa Amurka martani

Haramta shiga Amurka kan magudi: Ba zan amince da hakan ba - Gwamnan Kogi ya mayarwa Amurka martani

- Gwamnan jihar Kogi ya nuna bacin ransa kan abinda gwamnatin Amurka tayi masa

- Yanzu gwamnan da iyalansa ba zasu iya samun bizan shiga kasar Amurka ba

- Daga cikin wadanda aka kakabawa wannan takunkumi akwai Oshiomole da El-Rufa'i

Gwamnatin jihar Kogi ta aike wasikar martani ga gwamnatin kasar Amurka kan haramtawa gwamnan jihar, Yahaya Bello, shiga kasarta sakamakon zargin cewa ya yi magudin zaben gwamnan jihar a Nuwamban 2019.

A wasikar da ta aikewa Jakadan kasar Amurka a ranar 16 ga Satumba, 2020, gwamnatin ta ce kamata yayi Amurka ta baiwa gwamnan damar kare kansa.

Wani sashen wasikar da sakatariyar gwamnatin jihar SSG, Folashade Arike Ayoade ta aike yace: "Ba zamu amince da wannan ba. Idan da gaske kuna yi don gyaran demokradiyya ne, Akalla ya kamata ku ji daga bangarorin biyu ko ta yaya ne."

"Abinda kuka yi zai kara zuzuta jita-jita da karfafa masu yada labaran karya."

Gwamnatin tace duk da cewa an samu kalubale daban-daban a zaben gwamnan da aka yi bara, za'a yi gyara a zabuka masu zuwa.

KU KARANTA: Bayan shekaru 14 ana gini da rikicin hana ginawa, an kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a kasar Greece

Haramta shiga Amurkan kan magudi: Ba zan amince da hakan ba - Gwamnan Kogi ya mayarwa Amurka martani
Haramta shiga Amurkan kan magudi: Ba zan amince da hakan ba - Gwamnan Kogi ya mayarwa Amurka martani
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Anambra: ‘Yan Sanda sun kama wanda ake zargi ya kashe tsohuwarsa

Legit ta kawo muku rahoton cewa tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, na cikin wasu jiga-jigan siyasa a Najeriya da gwamnatin Amurka ta haramtawa shiga kasarta saboda zargin magudin zabe.

A ranar Litinin gwamnatin Amurka ta sanar da cewa ta haramtawa wasu yan siyasa a Najeriya shiga kasarta daga yanzu saboda zargin rashawa ko magudin zabe.

Rahoton da Sahara Reporters ta wallafa ya kara da cewa akwai sunan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; da gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Shi kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, an tsawaita haramtawar da akayi masa tun a baya.

A cewar jami'an kasar Amurka, za'a kara sunayen wasu yan siyasan Najeriya cikin jerin wadanda aka haramtawa shiga kasar bayan zaben jihar Edo idan sukayi magudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel