Zargin garkuwa da mutane: Alkali ya bukaci a adana masa mata da miji a gidan yari

Zargin garkuwa da mutane: Alkali ya bukaci a adana masa mata da miji a gidan yari

- Wata kotun majistare dake zama a jihar Benue ta bukaci a adana mata wani dan kasuwa mai suna Uttah Benjamin da matarsa Ada a gidan gyaran hali

- Wadanda ake zargin suna zaune ne a rukunin gidajen gwamnatin tarayya dake Makurdi, babban birnin jihar Benue

- Ana zargin ma'auratan da laifin garkuwa da mutane kamar yadda dan sanda mai gabatar da karar ya bayyana

Dan sanda mai gabatar da kara, Hyacinth Gbakor, ya sanar da kotu a ranar 12 ga watan Augusta 2020 cewa,wata Isiana Amarachi ta Oji River a jihar Enugu ta kaiwa 'yan sandan yankin 'C' a ranar 1 ga watan Augusta 2020, rahoton cewa wani ya saceta a Abuja kuma ya kaita wurin Uttah da Ada Benjamin a Makurdi.

Amarachi tace Ada tace mata zata zauna tare da ita har sai ta haihu. Ta kara da cewa Ada ta tabbatar mata da cewa, idan har na haihu za'a biyani N300,000.

Kamar yanda 'yan sanda suka bada rahoto, Amarachi taki yadda da tayin su kuma ta rokesu da su taimaka mata su saketa, amma sam suka tsoratar da ita da cewa zasu kasheta da jaririnta.

An kama ma'auratan da aikata laifin da yayi karantsaye ga sashi na 97 na dokar Penal code na jihar Benue, 2004 da kuma sashi na 3(2) akan sata, garkuwa da mutane da kuma kungiyar asiri da makamantan hakan na 2017.

Duk da wadanda ake zargin sun yita rokon sassauci. sai dai ba'a amince da hakan ba. Sannan lauya mai karesu A. A. Adenira ya roki bayar da belinsu, amma kotun sam ta ki amincewa da hakan.

Dama kuma an taba kama Ada da laifin garkuwa da jaririya 'yar wata 8 a Kadarko, jihar Nasarawa.

Kamar yadda 'yan sanda suka ruwaito, wata Mbalamen Dogo tana shagonta dake kasuwar Kadarko a inda take sayar da mangyada sai jaririnta ya fara rusa kuka.

KU KARANTA: Tirkashi: Sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa sun fara gudun ceton rai akan kisan Gana a jihar Benue

Zargin garkuwa da mutane: Alkali ya bukaci a adana masa mata da miji a gidan yari
Zargin garkuwa da mutane: Alkali ya bukaci a adana masa mata da miji a gidan yari. Hoto daga The Punch
Source: UGC

KU KARANTA: Tun bayan fitowa ta a fim a matsayin El-Zakzaky ana yi mini barazanar kisa - Cewar jarumi Pete Edochie

Tace, kwatasam sai ga wata mata ta shigo shagonta tace ta kawo jaririn ta tayata rarrashin shi, lamari da yasa ta mika mata jaririyar

Dan sanda mai gabatar da kara yace, bayan matar ta gama sallamar masu siyayyar da suka cika shagon sai ta farga matar nan tayi layar zana da jaririnta.

Ya kara da cewa, bincike ya tabbatar da cewa Ada ce wannan matar da ta sace jaririyar.

Mai Shari'ar kotun majistaren, Kor, ya bada umarnin cigaba da adana Ada a gidan gyaran hali, kuma ya daga zaman kotun zuwa 26 ga watan Oktoba 2020.

A wani labari na daban, bayan shekara daya da Gwamna Nyesom Wike ya sa kyautar Naira miliyan 30 ga duk wanda ya yi sanadin kama fitaccen dan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane, Honest Diigbara, wanda aka fi sani da Boboski, jami'an 'yan sanda sun damke shi.

Amma kuma kamun nashi bai zo da sauki ba, saboda sai da jami'an tsaro da 'yan sintiri a Korokoro da ke karamar hukumar Tai suka yi musayar wuta da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel