Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 7 a Kaduna, biyar daga cikinsu 'yan gida daya

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 7 a Kaduna, biyar daga cikinsu 'yan gida daya

- 'Yan bindiga sun kai hari garin Barakallahu a Kaduna sun sace mutum bakwai, biyar daga cikinsu 'yan gida daya

- 'Yan bindigan sun balle kofa sun shiga gidan wani Abdulsalam Haruna sun sace matarsa da yaransa hudu sannan suka shiga gidan makwabcinsa suka sace yara biyu

- Haruna ya ce sun kira jami'an tsaro amma ko da suka iso 'yan bindigan sun riga sun tafi da mutanen da suka sace

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 7 a Kaduna, biyar daga cikinsu 'yan gida daya
Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 7 a Kaduna, biyar daga cikinsu 'yan gida daya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

'Yan bindiga a safiyar ranar Juma'a sun sace mutane biyar 'yan gida daya da wasu mutum biyu a garin Barakallahu da ke jihar Kaduna kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Abdulsalam Haruna, mazaunin garin ya ce 'yan bindigan sun kai hari gidansa sun tafi da matarsa da yaransa hudu.

Ya kara da cewa sun afka gidan makwabcinsa nan ma sun yi awon gaba da yaransa biyu.

"Abin ya faru ne misalin karfe 1.30 na daren (Juma'a). Sun balle kofar gida na suka shigo harabar gidan. Sun balle kofar shiga dakuna suka tisa keyar kowa. Sun tafi da matata da yara na hudu, biyu cikinsu dalibai ne a Kwallejin Kimiyya da Fasaha na Tarayya da ke Malumfashi a jihar Katsina," in ji Haruna.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina

"Sun kuma kai hari gidan makwabci na sun tafi da yaransa biyu.

"Sun kuma afka wasu gidaje biyu, ciki har da gidan wani tsohon direkta a ma'aikatar ilimi na jihar Kaduna amma ba su tafi da kowa ba kuma ba su dauki komai ba a can.

"Mun sanar da jami'an tsaro amma a lokacin da suka iso 'yan bindigan sun tsere da wadanda suka sace."

Wannan na zuwa ne kimanin mako guda bayan da aka ruwaito cewa yan bindiga sace wasu 'yan gida daya su 17 a hanyarsu na dawowa daga gona a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikun.

An yi yunkurin ji ta bakin kakakin 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige amma hakan bai yi wu ba domin ba a same shi a waya ba a har lokacin da aka hada wannan rahoton.

A wani labarin daban, Jami'ai daga hedkwatan 'yan sanda da ke birnin tarayya Abuja sun kama daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a kan zargin yunkurin aikata kisan kai.

An ce wanda ake zargin, Sunday Okoro Ukwejemifor yana da hannu cikin yunkurin kashe wani dan kasuwa a garin Sapele mai suna Sunny Nwakego.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel