Yanzu-yanzu: FG ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan sanarwar cike sabon fom din banki

Yanzu-yanzu: FG ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan sanarwar cike sabon fom din banki

- Gwamnatin Tarayya ta bawa 'yan Najeriya hakuri bisa sakon da ta fitar a jiya Alhamis na cewa masu asusun bankuna su tafi banki su cike wani fom na musamman

- Gwamnatin ta ce an fitar da sakon ne a kan kuskure kuma ba batu ne da ya shafi kowa ba sai dai wani rukunin mutane da galibinsu ba 'yan kasa bane da masu wasu irin kasuwannci na musamman

- Sanarwar da gwamnatin ta fitar a jiya Alhamis ya fusata 'yan Najeriya da dama inda suka yi ta nuna bacin ransu a dandalin sada zumunta

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, FG, ta nemi afuwar 'yan kasar kan sanarwar da ta fotar na cewa dukkan masu asusun ajiyar kudi na banki su tafi bankunsu su karbi fom din kai-da-kai da za su cike.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin tarayyar ta fitar da sanarwa ta shafin ta na Twitter cewa dukkan masu asusun banki har ma da kamfanonin inshora za su cike wasu fom inda za su bayar da wasu bayannai a kansu.

Yanzu-yanzu: FG ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan sanarwar fom din cike bayanan banki
Yanzu-yanzu: FG ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan sanarwar fom din cike bayanan banki
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya

Gwamnati ta bada umurnin ne a ranar Alhamis duk da cewa masu asusun bankuna suna da lambar tantacewa na bankuna wato BVN da ke kunshe da muhimman bayanansu da kuma lambar dan kasa wato NIN.

Sanawar ya ce ya yi baranazar cewa duk wanda bai tafi ya cike fom din ba zai iya fuskantar hukunci da ya hada ta rufe masa asusun banki ko kuma cin sa tara.

Wannan sanarwar da gwamnatin ta bada ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta inda mutane da dama suka nuna rashin jin dadinsu game da batun da suke ganin kawai wahal da su za ayi.

Sai dai a ranar Juma'a gwamnatin ta fitar da wani sabon sanarwa inda ta nemi afuwar 'yan kasar a kan sanarwar da ta ce mai rikitarwa ne.

KU KARANTA: An cafke hadimin Gwamna Okowa da ya ɗauki hayar wasu su kashe wani ɗan kasuwa

"Muna neman afuwa bisa ga sakonnin da muka fitar a jiya game da batun cike fom. Sanarwar ba kowa ta shafa ba. Hukumar tattara haraji @firsNigeria za ta yi karin bayani nan gaba."

A sakon da FIRS ta fitar, ta ce wasu rukunin mutane ne kawai za su cike wannan fom din. Mutanen galibi ba 'yan kasa bane da kuma wasu da ke kasuwannci da suke biya wa haraji a sassan kasar daban-daban.

A wani rahoton daban, Fitaccen mai kudin duniya kamu mai tallafawa al'umma Bill Gates ya yi magana game da matakan da Najeriya za ta iya dauka domin tsamo 'yan kasar daga talauci.

An yi kisayin cewa a kalla 'yan Najeriya miliyan 82.9 suke rayuwa cikin talauci, hakan yasa aka yi wa Najeriya lakabi "babban birnin talauci na duniya".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel