Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai sabon hari Magumeri, sun halaka mutum 3

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai sabon hari Magumeri, sun halaka mutum 3

- Wasu mayakan Boko Haram sun kai wa kauyukan Gareri da Kuwami hari a karamar hukumar Magumeri ta jihar Borno

- Mayakan ta'addancin sun kai harin inda suka kashe rayuka uku a kauyen tare da raunata wasu mazauna yankin

- Jama'a sun tabbatar da cewa, dabarar tserewa zuwa cikin daji ce ta kubutar da yawancinsu daga hannun 'yan ta'addan

Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai wa wasu kauyuka biyu hari a garin Borno inda suka kashe a kalla mutum uku tare da raunata wasu.

Jaridar Sahara Reporters ta gano cewa, 'yan ta'addan sun kai hari kauyukan Gareri da Kuwami da ke karamar hukumar Magumeri ta jihar Borno.

Magumeri karamar hukuma ce da ke arewacin Borno, kuma tana da nisan kusan kilomita 40 daga Maiduguri, babban birnin jihar, inda ake fuskantar hare-hare.

Mazaunan yankin sun ce da kyar suka sha inda suka fada daji domin gujewa garkuwa da su.

"An kashe mutum biyu a Gareri yayin da mutum daya ya mutu a Kuwani sakamakon harin 'yan bindigar," wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar.

KU KARANTA: Jerin sunaye: Jihohi 15 da za su amfana da tallafin bayan korona - NEC

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai sabon hari Magumeri, sun halaka mutum 3
Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai sabon hari Magumeri, sun halaka mutum 3. Hoto daga Sahara Reporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga sun kutsa karamar hukumar Zango Kataf da ke jihar Kaduna inda suka kashe mutum biyu tare da kone gidaje masu tarin yawa.

Kungiyar jama'a mazauna kudancin Kaduna (SOKAPU), a wata takarda, ta ce, 'yan bindiga sun shiga kauyen Manyi-Mashin da sa'o'in farko na ranar Juma'a, kuma sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu kadarori.

Jami'ar yada labaran kungiyar, Luka Binniyat, tace mutum biyun da suka rasu sun kone kurmus a cikin gidansu.

Watan Satumba ta kasance ta zubar jini ce a yankin, The Nation ta wallafa. SOKAPU ta ce: "A sa'o'in farko na ranar Litinin, 11 ga watan Satumban 2020, 'yan bindiga sun kutsa kauyen Manyi-Mashin da ke gundumar Zamandabo a karamar hukumar Zangon Kataf.

"Ana zargin wasu Fulani makiyaya ne suka kai harin inda suka kone kusan dukkan gidajen kauyen tare da kwashe kadarori suka yi awon gaba da su.

"An kone mutum biyu a cikin gidajensu kurmus. Wadanda suka rasu sun hada da Cecilai, wata mata mai takaba mai shekaru 62 wacce ta bar yara 6 da kuma Iliya Sunday mai shekaru 56 wanda ya bar yara 8.

"Duk da cewa jami'an rundunar Operation Safe Heaven sun yi martanin gaggawa, 'yan bindigar sun gaggauta tserewa kafin isowarsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel