Manomi ya kashe dan acaɓa ya sayar da babur dinsa kan kudi N120,000

Manomi ya kashe dan acaɓa ya sayar da babur dinsa kan kudi N120,000

- Ƴan sanda a jihar Gombe sun cafke wani mutum da ya kashe ɗan acaɓa ya kuma siyar da babur ɗin sa

- Ƴan sandan sun kama Ephraim Kadiri mai shekaru 37 a duniya a wani otel da ya ɓoye bayan aikata laifin

- Fusatattun matasa a Gombe sun yi yunkurin kai hari hedkwatar ƴan sanda don nuna ɓacin ransu kan rashin barinsu su ɗauki mataki a kan Kadiri

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe a ranar Alhamis ta yi holen wani manomi mai shekaru 37 mai suna Ephraim Kadiri da ake zargi da kashe wani ɗan acaɓa a Gombe.

Da ya ke gabatar da wanda ake zargin a hedkwatar hukumar, kwamishinan ƴan sanda, Shehu Maikuɗi ya ce wanda ake zargin ya sace babur ɗin ɗan acaɓan ya sayar N120,000.

DUBA WANNAN: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

Manomi ya kashe dan acaba ya sayar da babur dinsa kan kudi N120,000
Manomi ya kashe dan acaba ya sayar da babur dinsa kan kudi N120,000. Hoto daga The Punch/Guardian
Source: Twitter

Maikuɗi ya ce an kashe ɗan acaɓan sannan aka sace babur ɗinsa inda ya ƙara da cewa da ƙyar ƴan sanda suka ƙwato wanda ake zargin daga hannun fusatattun mutane.

KU KARANTA: Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya

Kwamishinan ya ce, "Shi (Kadiri) ya kusa janyo mana fitina a jiya Laraba a Billiri. Matasa a Billiri sunyi yunƙurin kawo mana hari, sai da kwamandan yankin ya yi wa matasan jawabi ya kuma tuntubi masu ruwa da tsaki.

"Daga bisani mun aika jami'an mu zuwa Cham inda aka kama wanda ake zargin a otel amma ya ce ya siyar da babur ɗin a Lamurde."

Kazalika, ƴan sandan sun gabatar da wani ɗalibin makarantar sakandare na ajin ƙarshe, Babayo Yahaya mai shekaru 21 da tramadol 59 da Exole da kudi N400,000 da ya bawa yan sanda toshiyar baki.

"An kama Babayo Yahaya ne sakamakon ingantattun bayannan sirri. Bayan da aka masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kashe kimanin shekaru biyu yana dillancin miyagun ƙwayoyi ne a Gombe da kewaye," in ji shi.

A wani labarin, kun ji jami'an tsaro a Uganda sun bazama neman wasu fursunoni fiye da 200 da suka tsere daga gidan yari, sun shiga wurin ajiye makamai sun tube tufafinsu sannan suka bazama cikin daji a arewa maso gabashin kasar.

A kalla mutane uku - daya soja biyu kuma cikin fursunonin - sun mutu yayin musayar wuta da aka yi a cewar kakakin rundunar sojin kasar, Birgediya Flavia Byekwaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel