PDP ta yi babban rashi, wani makusancin Dogara ya koma APC

PDP ta yi babban rashi, wani makusancin Dogara ya koma APC

- Jigon jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, kuma makusancin Yakubu Dogara, Mohammed Misau ya sauya sheka

- Mohammed Misau ya tabbatar da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC a wata tattaunawa da aka yi da shi ta wayar tafi da gidanka

- Kamar yadda Misau yace, ba zai iya zuba ido a ci amanar jama'ar jihar ba bayan sun dauka alkwarin kawo sauyi

Wani babban dan jam'iyyar PDP mai suna Mohammed Misau, ya sauya sheka inda ya koma jam'iyyar APC a jihar Bauchi.

Misau, wanda ya taba wakiltar Bauchi ta tsakiya, makusanci ne ga tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Ya sanar da sauya shekarsa zuwa APC bayan ziyarar shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Juma'a da yayi.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tsohon sanatan yana daya daga cikin fusatattun jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Bauchi.

Sauya shekarsa tana da alaka da barakar da ke tsakanin Gwamna Bala Mohammed da Dogara kamar yadda aka gano.

Misau ya bayyana nadamarsa a kan rawar da ya taka wurin ganin nasarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar, kamar yadda yace an nuna wa jiga-jigan jam'iyyar iyakarsu da butulci.

Misau, wanda ya tabbatar da sauya shekarsa a wata tattaunawar waya da yayi da The Nation, ya ce: "Yadda Gwamna Bala Mohammed ke rike da jihar, babu yadda za a yi su zuba ido suna kallo.

"Bayan kuma mun daukar wa jama'a alkawarin ganin sauyi. Mun ce za mu yi fiye da gwamnatin da ta gabata amma sai ya fi wanda ya gabata lalacewa."

"Ina ta tattaunawa a kan sauya shekata. Kasa da minti 30 kenan da na bar jam'iyyar PDP na koma wurin dan uwana, Yakubu Dogara," yace.

Misau shine ya kula da taron PDP tare da shirya shi wanda aka yi a jihar Neja a makonni biyu da suka gabata.

Misau shine shugaban kwamitin samo kudaden da aka wawura na jihar, wanda Gwamna Bala Mohammed ya kafa na jihar Bauchi.

KU KARANTA: Soja da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wasika mai ratsa zuciya

PDP ta yi babban rashi, wani makusancin Dogara ya koma APC
PDP ta yi babban rashi, wani makusancin Dogara ya koma APC. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Tirkashi: Sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa sun fara gudun ceton rai akan kisan Gana a jihar Benue

A wani labari na daban, Daily Trust ta ce jam’iyyar PDP a jihar Bauchi ta na shirin yi wa tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara kiranye daga majalisar tarayya.

Idan ba ku manta ba, kwanan nan Yakubu Dogara ya fice daga PDP, ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin kasa da rinjaye a majalisar dokokin tarayya.

Rahotanni sun ce wannan sauya-sheka zuwa APC a karo na biyu da Yakubu Dogara ya yi, bai yi wa jam’iyyar PDP ta reshen jihar Bauchi da uwar jam’iyya ta kasa dadi ba.

Wani daga cikin manyan PDP a Bauchi, Malam Bibi Dogo, ya ce za su nemi shugabannin majalisar wakilai su janye kujerar Yakubu Dogara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel