Kano: Matar aure ta shake dan kishiya, ya sheka lahira ko shurawa babu

Kano: Matar aure ta shake dan kishiya, ya sheka lahira ko shurawa babu

- Hukumar NAPTIP, reshen jihar Kano ta damke Jamila Abubakar wacce ake zargi da shake dan kishiyarta har lahira

- Shugaban hukumar ya sanar da yadda suka gayyaceta watanni biyu da suka wuce aka ja mata kunne a kan cin zarafin yaron

- Bayan samun labarin kashe yaron da tayi, an aike da jami'ai inda suka cafkota tare da mika wa 'yan sandan jihar

Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa (NAPTIP), reshen jihar kano, ta cafke wata matar aure mai shekaru 29 mai suna Jamila Abubakar, kan zarginta da ake yi da kashe dan kishiyarta, Muhammad Bashir.

Shehu Umar, kwamandan NAPTIP na yankin, ya tabbatar da kamen a wata tattaunawa da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Alhamis a Kano.

Umar ya bayyana cewa, an kama wacce ake zargin a ranar Alhamis bayan ta yi wa dan mijinta mai shekaru 7 mugun duka har ya mutu a yankin Tarauni Kasuwa da ke birnin Knao.

Ya tunatar da cewa, NAPTIP ta gayyaci matar kusan watanni biyu da suka gabata a kan zarginta da ake yi da cin zarafin yaron.

Shugaban yace: "Mun samu bayanai da ke bayyana cewa da kyar aka kwace yaron a hannunta a watanni biyu da suka gabata. Kwatsam sai ga labarin shake shi da tayi har ya mutu.

"Babu kakkautawa muka tura jami'anmu wadanda duka damke matar da ake zargin."

Ya kara da cewa, binciken farko ya bayyana cewa matar ta saka yaron a daki inda ta hana shi abinci tare da hana shi walwalarsa ta yau da kullum.

"An gayyaci wacce ake zargin kuma an ceto yaron. Hukumar ta karbeshi tare da samar masa da magunguna sannan daga baya aka bai wa mahaifinsa.

"Sun rubuta yarjejeniya da mu a kan cewa ba za a sake tsaresa ba, kuma za su kula da shi tare da bashi kariya," yace.

Umar ya kara da cewa, tuni sun mika al'amarin gaban rundunar 'yan sandan jihar Kano domin ingantaccen bincike da gurfanarwa idan hakan ta kama.

KU KARANTA: Yadda wani biri ya saci wayar wani mutumi yaje ya dinga daukar hoto da bidiyo da ita

Kano: Matar aure ta shake dan kishiya, ya sheka lahira ko shurawa babu
Kano: Matar aure ta shake dan kishiya, ya sheka lahira ko shurawa babu. Hoto daga Solacebase
Source: UGC

KU KARANTA: Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi

A wani labari na daban, jami'an rundunar 'yan sanda na babban birnin tarayya Abuja sun samu nasarar ceto wasu yara guda biyu da ake zargin an rufe su a cikin bandaki a wani gida dake Garki cikin birnin na Abuja.

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Anjuguri Manzah, ya fitar ya ce, yaran guda biyu sun fuskanci cin zarafi daga wajen mutanen da suke rike dasu wadanda ke zaune a hawa na biyu daga cikin gidajen dake FCDA Quarters, Garki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel